An rufe makarantu saboda ƙarancin man fetur a Mali
[ad_1]
Duk makarantu a fadin ƙasar Mali da ke Yammacin Afirka za su ci gaba da kasancewa a rufe daga ranar 27 ga Oktoba zuwa 9 ga Nuwamba, sakamakon tsananin ƙarancin man fetur da ya janyo tsaikon harkokin sufuri da na yau da kullum.
Ministan Ilimi na ƙasar, Amadou Sy Savane ya sanar a ranar Lahadi cewa dukkan cibiyoyin ilimi za su dakatar da ayyukansu na tsawon makonni biyu saboda ƙarancin man fetur da ake fama da shi.
Amadou Sy Savane ya shaida wa gidan rediyon gwamnati na ORTM cewa an shirya sake buɗe makarantu a ranar 10 ga watan Nuwamba.
Tsawon makonni dai, Mali na fama da ƙarancin man fetur sakamakon toshe hanyoyin sufuri da kungiyoyin ‘yan bindiga ke yi, musamman hanyoyin da manyan motocin dakon mai ke bi zuwa babban birnin ƙasar, Bamako.
Wannan lamari kacokam shi ne ya haifar da dogayen layuka a gidajen mai, yayin da motocin haya da babura suka daina zirga-zirga, abin da ya sanya titunan Bamako da suka saba tumbatsa da ababen hawa suka yi tsit.
Haka kuma, jami’o’i da manyan makarantun gaba da sakandire a babban birnin sun dakatar da karatu saboda dalibai da malamai sun kasa isa makarantu ƙarancin man fetur.
A gefe guda kuma, Ofishin Jakadancin Amurka da ke Bamako ya sanar a ranar 24 ga Oktoba cewa ƙananan ma’aikatansa da iyalansu za su bar ƙasar saboda ƙarancin man fetur da yayin da kuma matsalolin tsaro ke ƙaruwa.
A Juma’ar da ta gabata ce kuma ofishin jakadancin ya bayyana cewa ba zai iya ci gaba da gudanar da ayyukansa na yau da kullum ko na gaggawa a wajen Bamako ba, tare da shawartar jama’a su ci gaba da bibiyar shawarwarin tafiye-tafiye da gwamnatin Amurka ke bayarwa game da Mali.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link