An kama ’yar Najeriyar da ta ɓoye hodar Iblis ta N195m a cikin burodi a Indiya

[ad_1]



An kama wata ’yar Najeriya, Olajide Iyanuoluwa, a ƙasar Indiya da gram 121 na hodar Iblis mai darajar kimanin Naira miliyan 195, da ake zargin ta ɓoye cikin burodi.

Hukumomin Indiya sun tsare Olajide mai shekaru 29 a kotu tare da fara shirin mayar da ita Najeriya.

A cewar jaridar The Indian Express a ranar Laraba, ’yan sandan jihar Karnataka ne suka kama Iyanuoluwa bisa zargin safarar hodar daga Mumbai zuwa Bengaluru.

Bincike ya nuna cewa wacce ake zargi ta isa Indiya a shekarar 2024 da izinin shiga kasar na dalibai, inda ta fara zama a Delhi kafin a kama ta.

Kwamishinan ’yan sandan birnin Bengaluru, Seemant Kumar Singh, ya ce an kama ta ne bisa sahihan bayanan sirri.

“Bisa bayanan sirri cewa wata baƙuwar mace da ke zaune a Grace Trust, cikin yankin ofishin ’yan sandan Varthur a Bengaluru, tana rarraba haramtacciyar kwayar cocaine ga wasu mutane, sai rundunar CCB Narcotics Control Wing ta kai samame,” in ji Singh.

Aminiya ta gano cewa yayin samamen da aka kai a ranar Talata, jami’an tsaro sun gano hodar iblis din daga wurin Olajide tare da kama wayar salula da wasu kayayyaki da ake zargin ta yi amfani da su wajen aikata laifin.

’Yan sanda sun ƙara da cewa duk da ikirarin Olajide na cewa daliba ce, bincike ya nuna ta zauna a wurare da dama a Mumbai, ciki har da Ghatkopar (Gala Nagar), Ambawadi da Nallasopara, “amma ba tare da ta yi rajista a kowace makaranta ba.”

A cewar Singh, binciken farko ya nuna cewa wacce ake zargi ta samo hodar ce daga abokinta a Mumbai, sannan bisa umarninsa ta kai wuraren da aka tsara.

Ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna ta yi tafiya daga Mumbai zuwa Bengaluru ta motar bas, inda ta ɓoye hodar a cikin burodi da makamantansu don kauce wa gano ta.

Rahoton ya ƙara da cewa bayan an kama Olajide, ’yan sanda sun kai samame a kusa da Varthur, inda aka kama wanda zai karɓi kayan.

Kama Olajide ya ƙara yawan jerin ’yan Najeriya da aka kama kuma aka mayar daga Indiya bisa laifin safarar kwaya.

Rahoton ya ƙara da cewa bayanan Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Indiya sun nuna cewa sama da baƙi 300, ciki har da ’yan Najeriya, aka mayar ƙasashensu saboda safarar kwaya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *