An kama mutum 5 da kuɗin jabu, bindiga da tumaki 180

[ad_1]



Rundunar ’yan sandan jihar Sakkwato ta kama mutane biyar da ake zargi da hannu a harkar kuɗin jabu, sannan ta ƙwato bindiga ƙirar AK-47 da tumaki 180 yayin wasu samame daban-daban da aka kai a faɗin jihar.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Ahmad Rufa’i ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, inda ya ce jami’an sashin yaƙi da garkuwa da mutane sun gano wata ƙungiyar masu kuɗaɗen jabu da aka sani da sunan “Sai Malam”.

A cewarsa, Jami’in ɗanda (DPO) na shiyyar Illela ya miƙa wasu mutane uku da ake zargi ga sashen binciken manyan laifuka (CID) domin gudanar da bincike, waɗanda suka haɗa da: Muhammad Hamidu daga Kwanni a Jamhuriyar Nijar, Umar Hassan da kuma Sadik Isah daga ƙaramar hukumar Illela.

Rufa’i ya ƙara da cewa, binciken sirri ne ya kai ga kama wasu ƙarin mutane biyu, Buhari Abubakar da Kasimu Muhammad, dukansu mazauna unguwar Makera Asada a cikin birnin Sakkwato. Ya ce rundunar ta yi nasarar ƙwato kudi na jabu da wasu kayan tsafi da ake amfani da su wajen gudanar da haramtacciyar sana’ar tasu.

A wani samamen na daban a ranar 10 ga Maris, sashin yaƙi da garkuwa da mutane na rundunar ya amsa kiran gaggawa game da wasu da ake zargi mambobin haramtacciyar ƙungiyar ‘Yan Sakai ne a ƙauyen Dakalo da ke ƙaramar hukumar Dange Shuni. Kungiyar, ƙarƙashin jagorancin wani Sani Nabuzuwa, ana zarginta da hannu a kisan kai da satar shanu.

“Ganin ’yan sanda ya sa maharan suka buɗe wuta, amma jami’anmu suka fatattake su inda suka tsere zuwa cikin daji,” in ji shi.

Kayan da aka ƙwato a wurin sun haɗa da: “Bindiga ƙirar AK-47, kunshi mai ɗauke da harsasai 11, tumaki 180 da ake zargin na sata ne, da kuma babur ƙirar Kasea.”

A gefe guda kuma, jami’an ofishin ’yan sanda na Arkilla sun kama wani matashi mai suna Auwal Sani daga ƙaramar hukumar Yabo, bisa zargin sojan gona.

Rundunar ta ce, wanda ake zargin da wani abokin aikinsa da har yanzu yake tsere, sun sanya kayan jami’an ’yan sanda na tafi-da-gidanka (MOPOL), inda suka tsayar da wani ɗan achaɓa sannan suka ƙwace babur ɗinsa ƙirar Boxer da sunan za su kai shi ofishin ’yan sanda.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ahmed Musa ya tabbatar wa mazauna jihar ƙudurinsa na kakkaɓe miyagu, sannan ya buƙaci jama’a da su ci gaba da bai wa rundunar bayanan sirri masu amfani.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *