An ji ƙarar tashin bama-bamai a Maiduguri
[ad_1]
Mazauna Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, sun shiga cikin firgici a yammacin wannan Litinin ɗin sakamakon ƙarar fashewar wasu abubuwa da ake zargin bama-bamai ne.
Aminiya ta ruwaito cewa ana zargin ’yan ta’addan Boko Haram ne suka tayar da bama-bamai a wasu sassan birnin.
Rahotanni sun ce mashigar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) da shatale-talen Kasuwar Monday da Elkanemi ne wuraren da fashewar ta shafa.
An samu rahoton cewa an ji ƙarar fashewa ta farko da misalin ƙarfe 7 na yammacin nan, jim kaɗan bayan da aka yi buɗa-baki.
Kawo yanzu dai babu tabbacin ko an samu asarar rayuka a lamarin wanda ya faru sa’o’i bayan da ’yan ta’adda suka kai hari a wani sansanin soji a Ajilari da ke wajen birnin Maiduguri, inda aka ƙona wata motar sintiri ta sojoji.
Sai dai sojojin sun yi nasarar daƙile harin tare da kashe wasu daga cikin ’yan ta’addan, yayin da da dama suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link