An Cire Tutar PDP A Fadar Gwamnatin Zamfara, A Shirin Sauya Sheƙa Zuwa APC
[ad_1]
An cire tutar PDP a Fadar Gwamnatin Jihar Zamfara da ke Gusau, yayin da mataimakin gwamnan jihar, Mummuni Bawa, ya jagoranci wasu manyan jami’an gwamnati zuwa jam’iyyar APC.
Mummuni, wanda aka zaba tare da gwamnan jihar, Dauda Lawal, a ƙarƙashin PDP a zaben 2023, na riƙe da muƙamin muƙaddashin gwamna a halin yanzu yayin da gwamnan yake ƙasar Saudiyya domin gudanar da Umrah.
- Sanata Barau Da Haɗin Kan APC A Kano
- Tinubu Ya Taya APC Murnar Nasara A Zaɓukan Birnin Tarayya, Kano Da Ribas
Rahotanni sun ce tun da fari a taron Majalisar Zartarwa ta Jihar, muƙaddashin gwamnan ya sanar da cewa manyan jiga-jigan PDP a Zamfara sun kammala shirin komawa APC.
A halin yanzu, Mummuni na gudanar da wata ganawa ta sirri da ‘yan Majalisar Dokokin Jihar a fadar gwamnati da ke Gusau, yayin da ake sa ran ƙarin bayani kan sauya sheƙar nan ba da jimawa ba.
Daraktan yaɗa labarai na fadar gwamnati, Salihu Anka, ya tabbatar cewa mambobin majalisar zartarwar gwamnan sun sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.
[ad_2]
Source link