Amina HOD Ta Sauya Sheƙa Zuwa APC, Ta Bayyana Goyon Bayanta Ga Gwamna Abba Kabir Yusuf

[ad_1]

Kwamishiniyar Harkokin Mata, Yara da Masu Buƙata ta Musamman ta Jihar Kano, Hajiya Amina Abdullahi Sani (HOD), ta sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC, inda ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da manufofinsa na bunƙasa Jihar Kano.

A wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar, an bayyana cewa Hajiya Amina HOD ta rungumi manufar “Kano Farko”, wadda ke da nufin ƙarfafa ci gaban jihar, zaman lafiya da haɗin kan al’umma. Sanarwar ta bayyana ta a matsayin ɗaya daga cikin fitattun jagororin mata da suka taka muhimmiyar rawa a tafiyar Kwankwasiyya a Kano da ma matakin ƙasa.

  • Ba Zamu Lamunci Buƙatar Murabus Ɗin Mataimakin Gwamna Ba — Kwankwasiyya
  • Yadda Buƙatun Kwankwaso Suka Tarwatsa Yiwuwar Haɗin Gwuiwa Da APC

Sanarwar ta ƙara da cewa sauyin sheƙar nata na daga cikin ƙarin goyon bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke samu daga manyan jami’an gwamnati da kwamishinoni, waɗanda suka tabbatar da biyayya da mara wa gwamnan baya wajen aiwatar da manufofinsa.

Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada cewa harkokin mulki na tafiya bisa tanadin doka, tana mai watsi da kalaman masu sukar gwamnati. Ta kuma tabbatar wa al’ummar Kano cewa za ta ci gaba da aiki da gaskiya da bin doka, tare da mai da hankali kan bunƙasa jihar da cika alƙawurran da aka ɗora mata.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *