‘Akwai ɗaliban da ke yin digiri yanzu ba tare da sun taɓa shiga ɗakin karatu ba saboda AI’
[ad_1]
Shugabar Cibiyar Nazarin Karatu da Ci Gaban Ilimi ta Najeriya (NCRRD) da ke Jami’ar Bayero Kano (BUK), Farfesa Amina Adamu, ta bayyana damuwa kan yadda dalibai ke ƙara gujewa amfani da dakunan karatu, tana danganta hakan da dogaro da kirkirarriyar fasaha ta AI.
Da take jawabi a taron ƙasa da ƙasa karo na biyar kan nazarin karatu da nazari da aka gudanar a Jami’ar Bayero Kano, Farfesa Amina ta ce da dama daga cikin ɗalibai yanzu suna kammala karatun jami’a ba tare da sun taɓa shiga ɗakin karatu ko sau ɗaya ba.
“Muna da daliban da ke yin rajista a shekarar farko kuma su kammala karatu ba tare da sun taɓa amfani da dakin karatu ko sau daya ba. Ba kamar da ba, lokacin da dalibai ke zuwa dakin karatu don neman bayanai da shiryawa jarrabawa, yanzu suna dogaro da fasajohin AI da sauran hanyoyin fasahar zamani,” in ji ta.
Farfesa Amina ta yi gargadi cewa duk da amfanin da AI ke da shi, tana haifar da abin da ta kira “lalaci a fannin yin tunani” a tsakanin dalibai.
“Suna saka duk aikin da aka ba su manhajar AI ta yi musu, sannan su miƙa amsar da suka samu ba tare da yin tunani da kansu ba. AI an ƙirƙire ta ne don taimakawa, ba don maye gurbin ƙirƙira da tunanin ɗan adam ba,” in ji ta.
Ta bukaci malamai, iyaye da sauran masu ruwa da tsaki da su rungumi AI da kansu, sannan su koya wa dalibai yadda za su yi amfani da ita cikin hikima.
“Ba za mu iya kawar da fuskarmu daga samuwar AI ba. Duniya na tafiya da ita, dole mu ma mu bi. Amma dole ne mu koya wa dalibai yadda za su yi amfani da AI ta hanyar haɗa amsoshin da ta bayar da nasu tunanin, ta hanyar yin nazari da zurfin tunani,” in ji ta.
Shi kuwa a nasa jawabin, Shugaban Jami’ar BUK, Farfesa Haruna Musa, ya bayyana cewa jami’ar na shirin kafa cibiyar nazari kan AI da da fasahar mutum-mutumi, inda ya ce nan ba da jimawa ba za a fara koyar da darussa kan fasahar zamani a cikin kundin karatun jami’ar.
“BUK ta shirya yin amfani da wannan fasaha don sauya tsarin karatu da bincike. Ba wai koyar da ita a matsayin darasi kaɗai ba, mun kuduri aniyar kafa cibiyar zamani ta AI da da fasahar mutum-mutumi. Taron yau ya nuna mana tasirin AI a fannin karatu, bincike da nazari,” in ji shi.
Ya kuma bukaci malamai da su yi amfani da fasahar don sauya tsarin koyarwa da koyo a makarantunsu, da nufin inganta ilimi ga yara da al’umma gaba ɗaya.
A jawabinsa na buɗe taro, Shugaban Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), Dr Aminu Maida, ya bayyana rawar da hukumar ke takawa wajen samar da kayan aiki da za su ba da damar amfani da AI a faɗin Najeriya.
Dr Aminu, wanda, Daraktan Bincike da Ci Gaban Fasaha a hukumar, Ismail Adedigba, ya wakilta, ya ce NCC a matsayin hukumar gwamnati da ke kula da harkar sadarwa a Najeriya, ta ƙaddamar da cibiyoyin fasahar zamani a Kano da Lumu don samar da ingantaccen yanayi ga ci gaban AI.
Ya bayyana cewa hukumar ta tallafa wa manyan makarantu guda shida da ayyukan binciken kan AI a shekarar 2024.
Adedigba ya kuma jaddada muhimmancin amfani da tsare bayanan masu amfani da intanet, inda ya ce NCC tare da Hukumar Kare Bayanai ta Najeriya suna aiki tare don tabbatar da tsaron bayanai a cikin tsarin AI.
Ya kuma ce shirin 3MTT na gwamnatin tarayya, wanda ke da nufin horar da ’yan Najeriya miliyan uku a muhimman fannonin fasaha ciki har da AI da tsaron intanet, tuni ya riga ya horar da sama da mutum 60,000 a cikin rukuni na farko, yayin da wasu rukunan ke tafe a nan gaba.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link