Aisha Buhari ta ziyarci Atiku a ƙasar Saudiyya

[ad_1]



Matar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta kai ziyarar ban girma ga tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar a ƙasar Saudiyya.

Uwargidan tsohon shugaban ƙasar ta samu rakiyar wasu ’yan uwanta har da ɗiyarta.

Atiku wanda ya wallafa hoton ziyarar a shafukan sada zumunta, ya ce ya ji daɗin wannan ziyara.

“An karrama ni ne, na karɓi baƙuncin Hajiya Aisha Buhari, matar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, da ’yarta Hanan, da sauran ‘yan uwa a ziyarar da suka kawo min a ƙasar Saudiyya, uwargidan tsohon shugaban ƙasa da danginta suna ƙasar Saudiyya don yin umara -AA”. Kamar yadda ya wallafa a shafinsa.

Atiku da Marigayi Buhari sun kasance manyan jiga-jigan siyasa waɗanda fafatawar su ce ta haifar da yanayin siyasar Najeriya shekaru da dama, inda suka fafata da juna a zaɓukan shugaban ƙasa daban-daban.

Duk da bambance-bambancen da ke tsakanin su na siyasa, mutanen biyu sukan fito fili suna bayyana rawar da juna ke takawa a tafiyar dimokuraɗiyyar Najeriya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *