‘A watan gobe fadar Aso Rock za ta cire kanta daga wutar lantarki ta koma sola’

[ad_1]



Babban Sakatare a Fadar Shugaban Ƙasa, Temitope Fashedemi, ya ce suna sa ran a watan Maris fadar ta Aso Rock za ta cire kanta gaba ɗaya daga layin wutar lantarki na ƙasa ta fara amfani da sola kacokam.

Hakan a cewarsa ya biyo bayan kammala aikin samar da wutar lantarki ta hasken rana da fadar ta samar a shekarar da ta gabata.

Temitope ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin kare kasafin kuɗin Fadar Shugaban Ƙasa na shekarar 2026 a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Musamman a majalisar dokoki ta ƙasa da ke Abuja.

Wannan bayani ya fito ne daga cikakken rahoton zaman kwamitin da fadar shugaban ƙasa ta aika wa manema labarai a daren Laraba.

Ya shaida wa kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Sanata Kaka Lawan (Borno ta Tsakiya), cewa an kammala shigar da na’urorin hasken rana a ƙarshen shekarar 2025 kuma ana gwada su tun daga watan Disamban na bara.

Ya ce, “Muna fatan watakila kafin watan Maris za mu iya komawa kanta kacokam,” inda ya ƙara da cewa wannan sauyi zai kawo gagarumin sauƙin kashe kuɗin wutar lantarki ga gwamnati.

Babban Sakataren ya kawo misali da Asibitin Fadar Shugaban Ƙasa a matsayin hujja kan ingancin komawa solar.

Ya ce asibitin ya kammala shigar da nata na’urorin hasken rana a watan Mayun 2025 kuma tun daga lokacin tana aiki ita kaɗai ba tare da amfani da injinan janareta ba.

Ya ce, “Dole ne in faɗi cewa tun daga lokacin, ba a sake kunna janaretan da ke Asibitin Fadar Shugaban Ƙasa ba, ko da na minti ɗaya, tun daga watan Mayun na bara.

“Sai dai a wasu watanni kaɗan, mun yi amfani da kashi uku cikin 100 daga Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC) sauran kuma daga hasken rana da tsarin ajiya na baturin lantarki.”

A shekarar 2025 ce Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 10 don aikin sauya fadar zuwa samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana.

Matakin dai a lokacin ya haifar da suka daga ’yan Najeriya da dama, waɗanda suka ce hakan tamkar amincewa ne cewa gwamnatin Tinubu ba za ta iya gyara matsalar wutar lantarki a Najeriya ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *