Gwamnatin Gombe ta fito da sabon tsarin yaƙi da cin zarafin yara da mata




Gwamnatin Jihar Gombe ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da cin zarafin mata da yara ta hanyar faɗaɗa dokoki ta hanyar wayar da kai da kuma aiwatar da dokar cin zarafinsu a faɗin jihar.

Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe, Hajiya Asma’u Muhammad Inuwa Yahaya, wadda Kwamishiniyar Harkokin Mata da Ci gaban Al’umma, Asma’u Muhammad Iganus, ta wakilta ce ta bayyana hakan.

Ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da cewa kowa ya fahimci Dokar Kare Yara da Dokar Hana Cin Zarafi (VAPP) da aka sanya wa hannu a ranar 14 ga watan Oktoban 2022.

A yayin jawabi a wani taron wayar da kai da tattaunawa a Gombe, Iganus ta ce rashin sanin doka a tsakanin al’umma na rage tasirin aiwatar da ita.

Ta jaddada cewa ba za a iya kare mutane ba sai sun fahimci haƙƙinsu da nauyin da ke kansu.

Ta ƙara da cewa tun bayan Gangamin Kwanaki 16 na Yaƙi da Cin Zarafi a bara, gwamnati ta kafa Kwamitocin Kare Yara a dukkanin ƙananan hukumomi tare da umartar su da su wayar da kan jama’a.

“Haka kuma, an zaɓi Jihar Gombe cikin jihohi shida da za su aiwatar da wannan shiri tare da haɗin gwiwar Dandalin Matan Gwamnonin Najeriya da Gidauniyar Ford,” in ji ta.

Kwamishiniyar ta bayyana cewa ma’aikatar na aiki tare da Cibiyar Karɓar Rahoton Cin Zarafi ta Jinsi (SARC) domin bai wa waɗanda aka ci zarafi kulawa da tallafi.

“Bayan jinya da shawarwari, ana kai su matsugunin ma’aikatar domin gyaran hali da koyon sana’o’i, sannan a haɗa su da Ofishin Uwargidan Gwamna domin samun tallafin dogara da kansu.”

Ta ce gwamnati ta haɗa sarakunan gargajiya, shugabannin ƙananan hukumomi, kansiloli, da shugabannin unguwanni a matsayin jakadu na musamman domin tabbatar da cewa saƙon ya isa kowane gida.

A nasa ɓangaren, Wakilin Babban Hakimin Birnin Gombe, Alhaji Sammani Bappah, ya bayyana taron a matsayin mai muhimmanci.

Ya ce yadda gwamnati ke tunkarar matsalar cin zarafi alama ce ta cikakkiyar jajircewa.

Ya kuma yaba wa ƙoƙarin kwamishiniyar, wanda ya sa Sarkin Gombe ya ba ta sarautar “Gatan Marayun Gombe”.

Shugaban Kwamitin Majalisar Dokoki kan Harkokin Mata, Hon. Gabriel Galadima, ya tabbatar da goyon bayan majalisar na kawo ƙarshen cin zarafi.

Kakakin Majalisar, Abubakar Muhammad Luggerewo, wanda Shugaban Masu Rinƙaye Ladan Gaule ya wakilta, ya buƙaci malamai da shugabannin addinai su ƙara wa’azi kan illar cin zarafi.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *