Wata mata ta tsere da motar saurayinta bayan sun kwana tare a wani otel da ke unguwar Asokoro a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

[ad_1]



Wata mata ta tsere da motar saurayinta bayan sun kwana tare a wani otel da ke unguwar Asokoro a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Aminiya ta ruwaito cewa mutumin, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya shiga otel ɗin ne tare da matar da yammacin Laraba.

Majiyoyi sun ce washegari da misalin ƙarfe 7:12 na safe, yayin da mutumin ke barci, matar ta shirya a hankali, ta ɗauki makullin motarsa, sannan ta nufi wurin ajiye motoci.

An ce ta fita da motar tana nuna kamar za ta je ta sayo wani abu ne a waje.

Bayan mutumin ya tashi barci, sai ya gano cewa matar da motarsa duk sun salwanta. Nan take ya sanar da jami’an tsaro.

An ce akwai muhimman takardu, kwamfuta laptop, da kuma kuɗi da ba a bayyana adadinsu ba a cikin motar lokacin da matar ta gudu da motar.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin.

Ta ce ’yan sanda suna bincike a halin yanzu tare da ƙoƙarin cafke wadda ake zargi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *