NiMet Ta Yi Hasashen Ƙwallewar Rana Da Gajimare Na Kwana Uku, Litinin – Talata

[ad_1]

Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa daga ranar Litinin zuwa Laraba za a samu rana da gajimare a sassa daban-daban na ƙasar. A cewar hasashen da ta fitar a Abuja, yankin Arewa zai kasance da rana da gajimare a duk tsawon kwanakin.

A yankin Kudu kuwa, ana sa ran za a samu rana tare da gajimare, tare da yiwuwar tsawa da ruwan sama kaɗan a wasu sassan jihohin Bayelsa, da Rivers, da Akwa Ibom da Cross River daga bisani a rana.

  • Za A Yi Ruwan Sama Na Kwanaki 3 A Jere A Wasu Jihohin Nijeriya – NiMet
  • Gyaran Dokar Zabe: Yadda Jinkirin Majalisar Dattawa Zai Iya Kawo Tsaiko Ga Zaben 2027

NiMet ta ce a ranar Talata, yankunan Arewa da Tsakiya za su fuskanci rana mai ɗan hazo, yayin da a Kudu ake hasashen tsawa da ruwan sama kaɗan da safe a jihohin Ogun, da Lagos, da Rivers, da Bayelsa, da Akwa Ibom da Cross River, sannan daga bisani a samu rana a wasu sassan Ondo, da Imo, da Delta da sauran jihohi.

A ranar Laraba, ana sa ran hazo da ƙura a Arewa, musamman da rana da yamma, yayin da a Tsakiya ma za a samu rana mai hazo. A Kudu kuwa, za a samu gajimare da rana tare da yiwuwar tsawa a jihohin Anambra, da Imo, da Abia, da Edo, da Bayelsa, da Delta, da Cross River, da Akwa Ibom da Rivers.

Hukumar ta shawarci jama’a, musamman masu fama da cututtukan numfashi, da su yi taka-tsantsan, tare da gargaɗin direbobi da matuƙan jiragen sama su nemi sahihan bayanan yanayi daga NiMet kafin gudanar da ayyukansu.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *