Jami’ar Umaru Musa Yar’adua ta karrama marigayi Buhari
Jami’ar Umaru Musa Yar’adua (UMYU) da ke Katsina ta bai wa marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, digirin girmamawa na digirgir wato Doctorate a fannin Kimiyyar Siyasa.
Wannan na zuwa ne a yayin bikin yaye ɗaliban jami’ar karo na 14 da aka gudanar a ranar Asabar a Katsina.
Majalisar Gudanarwar Jami’ar ta ce an karrama Buhari ne saboda gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban siyasar Najeriya, jagoranci na hangen nesa, da kuma ƙoƙarinsa na haɗa kan al’umma da bunƙasa ƙasa.
Da yake jawabi a madadin sauran waɗanda aka karrama, tsohon Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa (NIA), Ambasada Ahmad Rufa’i, ya shawarci ɗaliban da suka kammala karatu da su kasance masu kishin ƙasa, gaskiya da riƙon amana, tare da sadaukar da kansu wajen yi wa ƙasa hidima ba tare da gajiyawa ba.
Ambasada Rufa’i ya buƙaci ɗaliban da su yi amfani da ilimin da suka samu wajen gina al’umma mai bai wa kowa dama, inda ’yan ƙasa za su rayu cikin mutunci, zaman lafiya da samun ci gaba.
Aminiya ta ruwaito cewa, bikin ya shaida bai wa ɗalibai takardun shaidar digiri da difloma a sassa daban-daban na jami’ar, tare da karrama wasu mutane da lambobin yabo na girmamawa bisa gudummawar da suka bayar wajen ci gaban ƙasa.