Majalisar Dokokin Kano ta musanta yunƙurin tsige Mataimakin Gwamna

[ad_1]



Majalisar Dokokin Kano ta musanta rahotannin da ke iƙirarin cewa ana shirin tsige Mataimakin Gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam Gwarzo, tana mai bayyana hakan a matsayin zargin da ba shi da tushe balle makama.

Mai magana da yawun Kakakin Majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai, ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a Kano, a ranar Asabar.

A cewarsa, babu wata tattaunawa, ƙuduri ko yunƙuri a cikin Majalisar da ke nufin tsige Mataimakin Gwamnan.

Ya jaddada cewa rahotannin da ke yawo a wasu sassan kafafen watsa labarai ba su da inganci, kuma na iya haddasa tashin hankali da ruɗani a fagen siyasar jihar.

“Babu ko da ɗan ɓurɓushi na gaskiya cikin wannan iƙirarin. Majalisar ba ta fara ba kuma ba ta la’akari da wani yunƙuri na tsige Mataimakin Gwamna. Rahotannin ƙarya ne, kuma jama’a su yi watsi da su,” in ji Shawai.

Ya ƙara da cewa Mataimakin Gwamnan na ci gaba da gudanar da ayyukansa yadda ya kamata, tare da cikakken goyon bayan Majalisar Dokoki, saɓanin jita-jitar da ake yaɗawa.

Shawai ya kuma yi kira ga kafafen watsa labarai da al’umma da su riƙa taka-tsantsan tare da tantance sahihancin bayanai kafin wallafawa ko yaɗawa, yana mai cewa aikin jarida na gaskiya na taka muhimmiyar rawa wajen kare zaman lafiya a siyasance domin samun amincewar jama’a.

A cewarsa, Majalisar ta mayar da hankali kan ayyukanta na kundin tsarin mulki, ciki har da yin dokoki da sa ido kan ayyukan gwamnati, maimakon tsunduma cikin jita-jita marasa tushe.

“Babban abin da ya sa muka sa gaba shi ne nagartaccen shugabanci domin hidimta wa al’ummar Jihar Kano. Ba mu bai wa jita-jita ko zarge-zargen da ba su da tushe muhimmanci ba,” in ji shi.

Zuwa yanzu dai babu wani martani da Mataimakin Gwamnan ya mayar dangane da wannan zargin ba.

Sai dai majiyoyi sun tabbatar da cewa yana ci gaba da gudanar da ayyukansa na yau da kullum a hukumance.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *