Ban Taba Da-Na-Sanin Shiga Harkar Fim Ba —Rukayya
[ad_1]
Shafi ne da yake zakulo muku fitattun jarumai manya da kanana, daga cikin masana’antar shirya fina-finan hausa ta Kannywood. Kamar kowane maoo yau ma shafin na tafe da wata babbar jarumai wacce take taka rawa a yanzu wato, RUKAYYA IBRAHIM wacce aka fi sani da ASABEinda ta bayyanawa masu karatu batutuwan da suka shafi rayuwarta da kuma sana’arta ta fim, kana jarumar ta yi wani tsokaci ga masu yunkurin shiga cikin masana’antar Kannywood, musamman mata matasa masu tasowa.
Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar jaridar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA kamar haka;
- Kasar Sin Na Da Kayayyakin Tarihi Na Halittu Na Duniya Guda 15
- Ronaldo Ba Shi Da Ikon Yanke Hukunci A Gasar Saudi Pro League – Mahukunta
Da farko za ki fadawa masu karatu cikakken sunanki tare da sunan da aka fi saninki da shi.
Sunana Rukayya Ibrahim Sharada, wacce aka fi sani da Asabe a cikin shirin Garwashi.
Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
An haife ni a unguwar Gwale ‘yan Alewa, a nan na yi firamare, sai na tafi ‘Da’awa Secondary School’ a can ‘Railway’, na tsaya iya jiniyo. Sai aka yi min aure, ina da yarana guda biyar, uku maza, biyu mata. Dan babban yaro na ma ya yi aure har matar sa ta haihu.
Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma harkar fim?
Harkar tana ba ni sha’awa sosai, ina yawan kallon finafinan hausa ina jin dadi, dan ni fim din indiya ko america ba su fiya damu na ba, amma indai an ce hausa ne to zan kalla.
Za ki yi kamar shekara nawa da fara fim?
Zan yi kamar shekara takwas a kannywood.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
An sha gwagwarmaya sosai ba kadan ba.
Ya batun iyaye ko iyali lokacin da kika fara sanar musu za ki fara harkar fim, ko akwai wani kalubale da kika fuskanta daga gare su?
Na fuskanci kalubale sosai a wajen ‘yan’uwana da saurknsu, sun nuna ba sa so, ni tun da mahaifina yana so ban damu ba. Dan ni mahaifina ba abin da zan ce masa sai Allah ya saka masa da alkhairi, ya ba ni gudunmawa sosai akan harkar. Dan ni duk cikin ‘yan’uwana ma da yaron wajena su ne suka nuna kyamatar abun, amma mahaifina da kansa yake cewa ba matsala, “ubangiji Allah ya taimake ki”, na ce amin.
Da wanne fim kika fara, kuma ya karbuwar fim din ya kasance ga masu kallo?
Na fara da Dadin Kowa, a shi ne aka fara doran ‘camera’ a Arewa24. Na fito a babar Haidar, daga nan ne abu ya dora.
Kin yi finafinai sun kai kamar guda nawa?
Ba zan iya gane ko guda nawa nayi ba, saboda na yi su da yawa.
Ko za ki fadowa masu karatu sunayen wasu daga cikin finafinan?
Akwai; Dadin Kowa, Garwashi, Allura Cikin Ruwa, So Ne, Yaron Gida, Labarina, da sauransu suna da yawa gaskiya.
Wane fim ne ya zamo bakandamiyyarki cikin finafinan da kika fito, kuma me ya sa?
Garwashi shi ne dai muke ta fafatawa.
Ko akwai wani fim wanda ya baki wahala a lokacin da ake daukarsa, kuma me ya sa?
Shi ne ‘Bakon Harshe’ dan ba zan taba mantawa da shi ba, da kuma Sarauniyar Mata. Guda biyun nan tunda nake finafinai ban taba wanda ya ba ni wahala kamar su ba. Dan Sarauniyar Mata ma wani dutse da muka hau na gangaro na fado na kuje wajen yayi jini a gwiwata har yanzu tabon yana wajen, agogona ya cire da wata laya da na daura ita ma ta fita. Haka Bakon harshe karfe hudun dare muke zuwa mu dauki shirin nan, mu dawo gida ba mu yi bacci ba, mu sake komawa. Wallahi da na koma gida bayan mun gama aikin nan kwananmu bakwai sai da aka kara min ruwa wajen leda hudu.
Ko akwai wani fim wanda kika taba fitowa cikinsa daga baya kika yi da kin sanin fitowa cikinsa?
Ban taba da-na-sanin shiga wani fim ba.
Wane irin nasarori ki ka samu game da fim?
An samu nasarori sosai ba kadan ba, an samu nasarori.
Ko akwai wani kalubale da kika taba fuskanta a cikin masana’antar Kannywood tun daga farkon shigarki zuwa yanzu?
Shi daman dan’adam ba ya wuce kalubale, akwai kalubale a cikin kowacce sana’a, amma kuma akwai nasarorinta. To, kalubalen ba wasu masu yawa bane, tunda tsakanina da mutane akwai fahimtar juna.
Ya kika dauki fim a wajenki?
Na dauki fim sana’a me kyau babbar ma sana’a,
Mene ne burinki na gaba game da fim?
Kawai Allah ya ba mu sa’a, ya bullo.mana da ayyuka na alkhairi.
Ko kina da ubangida a cikin masana’antar Kannywood?
Ba ni da ubangida a ‘industry’.
Wadanne jarumai ne suke burge ki a Kannywood, kafin shigarki cikin masana’antar, kuma me ya sa?
Aisha dan Kano, Ibrahim Mandawari, irin mutane na da din nan suna burge ni sosai. Su nake kallo da irin aktin din da suke yi yana burge ni. Saboda kalaman da suke fada da fadakarwar da suke yi.
Idan aka ganki a fili wadanne irin tambayoyi mutane suke yi miki?
Ina shan tambayoyi, ana ganina za a ce ga babar Atika can, ko maman Bala ta cikin fim din Labari na.
Ko akwai wani gyara ko ci gaba da kike ganin ya kamata a kawo shi cikin masana’antar Kannywood?
Bai wuce hadin kai ba, ya zamana mun zama tsintsiya daya, madaurinki daya. Ni shi nake so, tunda gabadaya sana’ar mu daya. Ya kamata idan daya ya ga daya, misali za ka ga jarumar da ta yi fuce ta ci karo da jaruma amma ba za ta iya yi wa na kasa magana ba. Ni shi ne yake damu na. Wannan gyaran nake so a kawo, idan jarumi ya ga jarumi dan’uwansa yayi masa magana tunda duk dodo daya mukewa tsafi sana’ar mu daya. A rika gaisawa da juna ana ci gaba da mu’amala da juna, dan wasu ba sa yi.
Wane kira za ki yi ga masu kokarin shiga masana’antar Kannywood?
In dai ba wai mace ta yi aure ta fito bane ba, ni ba na son na ga yarinya ba ta yi aure ba tana budurwa ta fara harkar fim. Saboda in ta ji dadin kudi to, ba za ta yi wannan auren ba. Kuma in za su shiga su tabbatar ‘yan’uwansu sun sani da duk dokokin da masana’antar ta kafa ya kamata ace mutum ya san wannan.
Ko kina da wani kira ko jan hankali ga sauran abokanan sana’arki na kannywood?
Mu hada kanmu dan Allah, duk abin da za mu yi a rayuwa to, mu hade kanmu. Shi ne za mu cimma gaci.
Bayan fim kina wata sana’ar ne?
Ina sana’o’ina a cikin gida, atamfofi da shaddodi, da mayafai da Hijabai duk ina siyarwa.
Ko kina da wadanda za ki gaisar?
Ina yi wa masoyana fatan alkhairi, ina yi wa iyayena fatan alkhairi, da sauran ‘yan’uwana da yayye na, da kannena, da ‘yan’uwana maza da mata. Ina yi wa kowa fatan alkhairi musamman mahaifina ina gaishe shi da kyau. Ubangiji Allah ya sa ya gama da duniya lafiya.
Me za ki ce ga masoyanki masu kallon finafinanki?
Su ci gaba da kallo kuma Allah ya saka musu da alkhairi, sai da su za mu ci gaba. Idan babu su ba a sanmu ba. Mun godewa Allah, ina yi wa masoyana fatan alkhairi masu kallon finafinamu Allah ya saka musu da alkhairi, Allah ya bar zumunci.
Muna godiya da bamu lokacinki
Ni na tafi.
[ad_2]
Source link