Ayyukan ‘Yan Daba A Kano: Kira Ga Shugabanni Da Malamai Da Masu Fada A Ji
Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu.
Musamman kasar mu ta Nijeriya, kasar mu ta gado, ke ba za a fita ba, kuma ba za a barki ba. Da za a raba gado, kowa sai an bashi nasa rabon. To, a nan aka haife mu, kasar mu ce, babu yadda za mu yi.
- Aisha Buhari Ta Ziyarci Atiku A Saudiyya
- Kasar Sin Na Da Kayayyakin Tarihi Na Halittu Na Duniya Guda 15
A wannan mako zan yi magana musamman a arewacin Nijeriya, mu hausawa akwai abubuwan da suke ta faruwa. Idan aka dauki harkar kwacen waya da harkar daba da ‘yan shaye-shaye na kananan yara to, fa dole mu dauki ragama ta inda muka fi karfi a wannan al’amari.
Dole babu yadda za ka yi baka isa ka ce ba mu muke kwacen waya da dabace-dabace ba, yaro dan kankani yanzu-yanzu zai burma maka wuka ya karbi waya to, mun fi kowa kwarewa akan irin wannan, kuma mun kasa daukar mataki akai.
To, magana ta gaskiya wannan kwacen waya da wannan kashe-kashen da yake ta faruwa idan har ana so a ga daidai, shugabanni nake magana masu mulki, ‘yan siyasa, masu kudi manya, masarauta masu fada a ji. Wallahi dole sai mun dawo kan gabar duk mutumin da ya kashe kawai a kashe shi, “Wannafsi Binnafsi” haka Allah ya fada.
Dole a kashe wanda ya kashe, yara kananan ‘yan shekara sha bakwai, sha takwas, suna ta kashe mutane, su kwace waya da sauransu. Kwanakin baya ana ta yin irin wannan kashe-kashen kuma ba wai bakon abu bane a Jihar Kano, wannan ya kashe wancen, wancen ya kashe wannan, ‘yan kananan yara malamai a makaranta su kashe su, ba a daukar mataki.
Yanzu da a ce shugabanni suna tsayawa tsayin daka duk wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wani shi ma sai an kashe shi, wallahi tallahi wani da za a bashi wuka ace burmawa wannan, wallah ba zai kashe shi ba. Ka ga mutum a waya cikin duhu yana tafiya a ce kwace ka buga masa makami, ba za ka buga masa ba. Amma yanzu mutum ne ya kashe yafi mutum goma an kama shi wata shida, bakwai an sako shi, ko shekara daya, biyu an sako shi, kumawa zai yi. Ko kuma wani ya gani ma ya ce wannan fa har ya fito to, zai aikata abin da ya aikata.
A kwanakin baya wasu sun je sun haura gida sun kashe iyali guda, shekarun baya wani malami ya je ya kashe wata yarinya gunduwa-gunduwa ya saka ta a buhu, ba a kashe su. Idan da hukuma za ta rika yanke hukunci wadanda suke aikata laifuka to, da masu kokarin aikata laifukan da ba su aikata ba.
Wallahi dole mu tsaya, dole shugabanninmu su tsaya su mayar da hankali akan wannan al’amarin, gudun abubuwan da suke fara faruwa a ‘yan kwanaki biyun nan. Wani ya saci waya an kama shi an kona shi, kada a fara daukar mataki a hannu ba zai haifar da da me ido ba, domin hakan zai haifar da fitina.
Ina kira ga shugabanni da malamai da duk masu fada a ji, su yi kokari su sanarwa shugabanni wannan hukuncin da ya kamata a rika dauka, domin Allah ne ya fada duk wanda ya kashe a kashe shi. Idan da mun bi abin da Allah ya ce, duk da ba mu samu wadannan kurakuren da ake aikatawa ba. Shi kansa wanda aka yankewa hukuncin ai ya samu sauki, domin ka yi masa hukuncin da ba sai an je gaban Allah ba. “_Wa nan katalamumidan mutahamidan Kadi ja’ahu jahannama khalidina fiha abada_”. In ka yanke masa hukunci kila ya samu sassauci, saboda an yi masa hukunci daidai da abin da Allah ya ce, in kuma ba haka ba to, jahannama za ka kai shi.
Dole ne iyaye su ma su dage da yi wa ‘ya’yansu addu’a, ka ga yaro baki babu dadi. In ka ga yaro na aikata abubuwa dole ne ka tsaya tsayin daka domin ganin wannan yaro ya daina, maganar soyayya ka kyale ta in ba haka ba, a hakan za su kare din. Kodai su kwaci waya a kone su ko kuma hukuncin ya rika kamawa ana kashe su. Kiri-kiri yaronka zai tashi ya shekara ashirin kana bauta masa kana yi masa wahala, in ba ka tsaya tsaya tsayin daka ba hannunka a banza a wofi.
Allah ya sa mu dace, Allah ya shirye mu baki daya, Allah ya yi mana maganin wannan musiba da ta taso mana.