Rigakafin Cutar Shanyewar Barin Jiki

[ad_1]

Fitacce, kuma kwararren likitan kwakwalwa da fyarfyadiya da ciwon kai da cutar shanyewar barin jiki da kuma sauran wasu cututtuka, sannan kuma Tsohon Shugaban Asibitin Gwamnatin Tarayya na Azare da ke Jihar Bauchi, Dakta Abdullahi Ibrahim ya bayyana yadda za a iya yin rigakafin cutar shanyewar barin jiki.

Masanin ya tabbatar da cewa, wannan cuta ta shanyewar barin jiki; kashi 75 cikin 100 na afkuwa ne sakamakon hawan jini, ma’ana dai hawan jini ne ke kawo cutar. Har ila yau, rigakafin cutar ita ce; kula da gwajin jini lokaci zuwa lokaci tare kuma da bin ka’idojin da likita ya gindaya da kuma motsa jiki yadda ya kamata.

  • Kimiyya Da Fasaha Na Da Amfani Amma Dalilin Raya Su Ya Fi Su Muhimminci
  • Shugabancin Ƙungiyar Kasuwar Singa (SIMDA) Ya Karyata Rahoton Tashin Sabuwar Gobara A Kasuwar

Babu shakka, wadanan hanyoyi su ne hanyoyin rigakafin wannan cuta ta shanyewar barin jiki da ke addabar al’umma a halin yanzu. Saboda haka, wajibi ne a kula kwarai da gaske, a kuma kiyaye da sauran cututtuka kamar irin su fyarfyadiya, ciwon kai mai zafi da sauran makamantansu, musamman ta hanyar zuwa asibiti, domin ganin likita tare kuma da shan magani a kan lokaci kamar yadda likita ya bayar da umarni.

Har ila yau, ya yi amfani da wannan dama wajen jawo hankalin al`umma cewa, an shiga wani irin yanayi a halin yanzu da ake bukatar kasancewa cikin yin addu’a a kowane lokaci. Kazalika  kuma, akwai bukatar mutane su rika yin tanadi; duba da yadda abubuwa suka canza tare da yin tsada, sanin kowa ne harkar lafiya a wannan lokaci ta yi matukar tsada; don haka, ya zama dole mu ririta lafiyarmu tare kuma da yi mata tanadi, saboda gudun bacin rana.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *