Masu Ruwa Da Tsaki Sun Gudanar Da Taro Kan Yadda Za A Tunkari Kakar Noman Bana
[ad_1]
Hukumar Bunkasa Aikin Noma ta Kasa (NADF), ta fara gudanar da nazari a kan kashi na farko, na yadda shirinta zai kasance kan samar da kayan aikin noma na bana.
Ta kuma yi alkawarin magance gibin da ake samu na samar da kayan aikin noma a kasar da kuma kara karfafa fannin aikin noman kasar a kakar noma ta bana da muke tunkara.
- Yadda Jihohi Bakwai Da Murtala Ya Kirkiro Suka Kasance Bayan Shekara 50
- Arewa Maso Gabashin Jigawa: Abokan Babandede Sun Dauki Harama
An gudanar da wannan nazari ne, a taron masu ruwa da tsaki a fannin na aikin noma, wanda kuma ya samu halartar wasu manoma da masu sarrafa amfanin gona da kuma kwararru.
Taron ya mayar da hankali ne, kan duba kan sakamakon da aka samu tun bayan kaddamar aikin na zango na daya.
Kazalika, an gudanar da shi ne, bisa nufin lalubo da mafita kan kalubalen da shirin ya fusknata a baya, musamman na sauyin yanayi, domin fara shirin tunkarar shirin zagaye na biyu.
An dai kaddamar da shirin ne, da nufin samar wa manoma ingantattun kayan aikin noma, domin su kara bunkasa aikin nomansu, musaman kananan manoman da ke cikin fadin kasar nan.
A jawabinsa a Abuja, a madadin hukumar ta NADF, Babban Sakare a hukumar, Mohammed Ibrahim Nasir Ingawa, ya bayyana cewa; an samar da shirin ne, domin dakile kalubalen da fannin aikin na kasar ke ci gaba da fuskanta da kuma samar da ingantattun kayan aikin noma ga manoman kasar, musamman a kan lokaci.
“Muna sane da wannan shirin da aka kaddamar tare da sanin kalubalen da ake fuskta, domin wadannan kalubale a zahirance suke, musmman a bangaren wanzar da duk wani abu da ya shafi samar da daukin ga fannin aikin noma,“ in ji Ibrahim.
“Kayan aikin noma da hukumar ta NADF ke samarwa a karkashin wannan shiri, wanda kuma ya kasance wata dabara ce da nufin kara samar da kayan aikin, musamman domin a kara habaka samar da amfanin gona mai tarin yawa ga kananan manoman da ke zaune a karkara,” a cewar Ingawa.
A cewar tasa, manyan nasarorin da aka samu a lokacin da aka kaddamar da shirin, sun hada da samar manyan aikin noma da rage kalubalen sauyin yanayi da ke zama babbar illa ga fannin na aikin noma a fadin kasar.
Ya ci gaba da cewa, aikin da za a gudanar a nan gaba, za a mayar da hankali ne wajen tabbatar da samar da ingantattun kayan aikin noma ga matasa da samar da kayan aikin noman rani, musamman domin a rage asarar da manoman kasar ke tafkawa, musamman bayan sun yi shuka.
Shi ma a nasa jawabin, wani mai sarrafa amfanin gona, Farfesa
Mukhtar Yusuf Abdullahi, ya sanar da cewa; wannan shirin, zai taimaka matuka, wajen rage kalubalen da manoman kasar ke fuskanta a fannin.
Sai dai, ya yi gargadin cewa; ana fuskantar matsaloli kan yadda ake shigo da kayan abinci cikin kasar nan daga kasashen ketare, wanda hakan ke haifar da tarnaki ga fannin aikin noman kasar.
Shi kuwa, wani wanda ya halarci taron Abubakar Said Dansadau ya sanar da cewa; tattaunawar na da matukar muhimmanci, sannan kuma ya kamata a ci gaba da gudanar da irinta a-kai-a-kai, musamman domin cimma burin da aka sanya a gaba.
[ad_2]
Source link