Mutum biyu sun mutu a rijiya a Kano
Akalla mutane biyu ne suka mutu a cikin rijiya wani bincike da aka yi a wasu unguwannin ƙananan Hukumomin Ungogo da Karaye a jihar Kano.
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce sashin bayar da agajin gaggawa ya samu kiran gaggawa kan samun ƙararrakin guda biyu a ranar Alhamis 5 ga Fabrairu, 2026.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Saminu Yusif Abdullahi ya fitar lamarin na farko ya faru ne a Bachirawa, Kwanar Madugu, a ƙaramar hukumar Ungogo.
A cewar sanarwar, hukumar kashe gobara ta samu kiran gaggawa daga Sulaiman Abdullahi Tela, bayan da wani matashi ɗan shekara 18 mai suna Yusif Malam Gwani Isah ya faɗa cikin wata buɗaɗɗiyar rijiya.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Ba tare da ɓata lokaci ba aka tura tawagar masu aikin ceto daga hedikwatar hukumar zuwa wurin, da isar su sai jami’an tawagar suka shiga cikin rijiya inda suka ɗauko wanda faɗa a sume, daga bisani kuma aka tabbatar da mutuwarsa.”
Ya ƙara da cewa, daga bisani an miƙa marigayin ga Hakimin unguwar Bachirawa, Jibrin Isah.
Lamarin na biyu ya faru ne a Kofar Yamma, cikin garin Karaye, cikin ƙaramar hukumar Karaye.
Sanarwar ta ce ofishin Hukumar kashe gobara reshen Karaye ta samu kiran gaggawa daga wani ma’aikacin Hukumar, PFS II Murtala Magaji, inda ya bayyana cewa wani yaro ɗan shekara takwas mai suna Abdussalam Ibrahim ya faɗa cikin rijiya.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Nan da nan aka tura tawagar masu aikin ceto reshen Karaye zuwa wurin, an ceto yaron daga baya aka tabbatar da mutuwarsa.
Daga baya an miƙa yaron ga mahaifinsa Malam Musa Mudi.
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta jajantawa iyalan mamacin tare da yin kira ga jama’a da su ɗauki matakan kariya a kewayen buɗaɗɗun rijiyoyi da magudanan ruwa, musamman don kare yara.