Yadda za a rabu da kaushi da faso a lokacin hunturu

[ad_1]



Tafin kafarmu na daya daga cikin abin da ya kamata mu rika kulawa da su a kowane lokaci. Domin idan ba a yi hanzari an magance wannan matsalar ta kaushi ba, sai ya zarce ya zama Faso.

Ta yaya mutum zai gane cewa yana da kaushin kafa? A lokacin da ya fara jin tafin kafarsa na janyo audugar jikin kujerar dakinsa ko kuma ya kama kaya ko ya kwarzani jikinsa, wannan shi ne kaushin kafa.

Mutane da dama na son rabuwa da wannan matsalar don haka musamman a lokacin hunturu, shi ne na kawo muku hanyoyi da za a bi don rabuwa da Kaushi.

A sami ruwan dumi sai a sanya a robar wanka sannan a rufe kafar ta dan jiku kadan. Sai a ajiye tawul a gefe.

Bayan tafin kafa ya jiku, sai a cire ta daga ruwan dumin, sannan a dauki dutsen goge kafa sai a goge inda ta yi kaushi, na zagaya dutsen a inda kaushin ya fito.

Sannan sai a sake mayar da kafar cikin ruwan dumi.

Bayan mintuna 15 sai a sake goga tafin kafar da dutsen goge kafa domin cire fatar da ta mace daga tafin kafa.

Daga nan sai a wanke tafin kafar da sabulu a cikin ruwa.

Sai a cire kafafun a goge su a jikin tawul domin su bushe.

A sami man shafawa a shafa a tafin kafa, idan ba a da shi, ko man basilin za a iya amfani da shi.

Sai a sami leda a sanya kowace kafa a ciki tare da sanya safa a tafin kafa kafin a kwanta bacci da dare.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *