Yadda Jihohi Bakwai Da Murtala Ya Kirkiro Suka Kasance Bayan Shekara 50

[ad_1]

A ranar 3 ga Fabrairu, 1976, kwanaki goma kacal kafin kashe shi, Nijeriya ta shaida daya daga cikin muhimman lokuta a tarihinta na tsarin mulki. Gwamnatin soja ta Janar Murtala Ramat Mohammed ta sanar da kirkirar sabbin jihohi bakwai, lamarin da ya fadada tarayyar kasar daga jihohi 12 zuwa 19 tare da sauya tsarin siyasa da rarraba yankunan kasar gaba daya.

An sanar da wannan matsaya ne ta hanyar shirye-shiryen rediyo a fadin kasar, mataki ne mai karfafa gwiwa, mai zurfin tasiri, kuma wanda ya bayyana salon shugabancin Murtala Mohammed sarai.

  • Rikicin Iran Da Amurka: Gabas Ta Tsakiya Ta Ɗauki Zafi
  • Taron Cika Shekaru 55 Na “Diflomasiyyar Ping-Pong” Ta Sin Da Amurka Ya Gudana A Amurka

An san shi da kasancewa mutum mai yanke hukunci cikin gaggawa, mai daukar gyare-gyare da muhimmanci, kuma wanda ba ya hakuri da jinkiri. Duk da cewa bai shafe fiye da watanni shida a mulki ba, kuma aka katse rayuwarsa kwanaki kadan bayan haka, wannan aiki ya zama daya daga cikin manyan abubuwan da suka bar tarihi a gajerce amma mai tasiri.

Jihohin bakwai da aka kirkira a wannan lokaci su ne Bauchi, Binuwe, Borno, Imo, Neja, Ogun da Ondo. Masana tarihi na ganin cewa hadin wadannan jihohi bakwai ya kasance wani yunkuri ne na magance dogwayen koke-koken al’umma na neman kusancin shugabanci, rage karfin ikon tsoffin yankuna, da kuma gina tarayya mai daidaito ta hanyar rarraba iko da mulki a matakin jihohi.

Janar Murtala Mohammed ya bayyana dalilansa a fili. A lokacin da yake sanar da shirin kirkirar sabbin jihohi, ya yi hujjar cewa girman Nijeriya, bambancin al’ummarta da tarihinta sun sa yawan tara iko a wuri guda ya zama ba wai rashin inganci kadai bane, har ma abin da ke da hadari.

A cewarsa, manyan yankuna sun yi nisa sosai daga jama’ar da suke mulka, lamarin da ke haifar da jin an ware su, rashin daidaiton ci gaba da kuma tashin hankalin siyasa.

A ganinsa, kirkirar jihohi ba kawai gyaran tsarin mulki ba ne, illa wani muhimmin kayan gina kasa. Ta hanyar kusantar da jama’a ga gwamnati, an sa ran sabbin jihohin za su inganta ci gaba mai adalci, karfafa hadin kan kasa da kuma rage rinjayen kabilanci da yankuna a cikin tarayya. Ya jaddada cewa za a fi samun dorewar hadin kan Nijeriya ba ta hanyar tilas ko yada kalamai ba, sai dai ta hanyar adalci, hada kowa da kowa da kuma daidaituwar tsarin gudanarwa.

Wannan tunani ne kuma ya jagoranci wani babban mataki da aka dauka kusan a lokaci guda, wato dauke Babban Birnin Tarayya daga Legas zuwa Abuja.

Murtala ya lura cewa Legas, baya ga cunkoso da matsin da ta ke fuskanta, ko alama ba ta dace ba, ta fuskar wasu alamomi da wurin zama a matsayin babban birnin kasa. Matsayinta na bakin teku, rinjayen wata kabila, da matsanancin matsin ababen more rayuwa sun sanya ta, a cewarsa, “ba ta cancanta ta zama Babban Birnin Tarayya ba.” Abuja kuwa, akasin haka ce, domin tana tsakiyar kasa, ba ta da yawan jama’a, kuma ba ta dauke da ikirarin kabilanci ko addini da ake dangantawa da tsofaffin birane.

An tsara ta ne a matsayin babban birni na tsaka-tsaki da zai kasance mallakin dukkan ‘yan Nijeriya ba tare da banbanci ba.

A dunkule, kirkirar sabbin jihohi da kuma yanke shawarar gina Abuja sun nuna hangen nesa daya da nufin samar da tarayya mai daidaito, rarraba iko, da hada kowa da kowa a Nijeriya.

Abin da ya sa aikin ranar 3 ga Fabrairu, 1976 ya zama na musamman a tarihi shi ne, lokacin da aka sanar da shi. An bayyana shi ne kwanaki goma kacal kafin a kashe Janar Murtala Mohammed a ranar 13 ga Fabrairu, 1976, a yayin wani yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba a Legas. A lokacin, yana da shekara 37 kacal, kuma bai shafe fiye da watanni shida a kan karagar mulki ba.

Saboda haka, jihohin bakwai na ci gaba da kasancewa a yau a matsayin hujjoji masu gamsarwa na wani zamani na shugabanci da bai ta’allaka ga tsawon lokaci ba, sai dai ga karfi, azama da tasirin ayyuka.

Bayan kisan Janar Murtala Mohammed, an nuna fargaba cewa da yawa daga cikin shirye-shiryensa za a iya soke su ko a watsar da su. Sai dai magajinsa, Janar Olusegun Obasanjo, wanda shi ma babban jigo ne a waccan gwamnatin, ya zabi bin tafarkin ci gaba da tsare-tsaren da aka fara. Ya bar jihohin bakwai yadda suke, ya ci gaba da aikin gina Abuja, sannan ya aiwatar da shirin sauya mulki da ya kai ga komawar mulkin farar hula a shekarar 1979.

Wannan ci gaba da aka samu ya tabbatar da cewa shawarwarin da aka yanke a ranar 3 ga Fabrairu, 1976 sun samu cikakken matsayi a tsarin kasa, da ba a bar su a matsayin ra’ayoyin da ba a kammala na wani shugaba da aka rasa ba.

Yadda aka kirkiri jihohi 7 a Nijeriya

Bincike ya nuna cewa kowacce daga cikin jihohin bakwai da aka kirkira a shekarar 1976 ta samo asali ne daga yanayi na tarihi da tsarin gudanarwa na musamman.

Misali, jihohin Bauchi da Borno an fitar da su ne daga tsohuwar Jihar Arewa maso Gabas (North-Eastern State), lamarin da ya kawo karshen shekaru masu yawa na tara iko a wuri guda a wani yanki mai fadi da ke cike da bambancin al’umma. Wannan rarrabuwa ta ba da damar gudanar da mulki cikin mai da hankali da kuma inganta isar da ayyukan gwamnati a yankin da ke da fadin kasa sosai.

Jihar Binuwe kuwa ta samo asali ne daga tsohuwar Jihar Binuwe-Filato, inda hakan ya ba yankunan da kabilar Tib ta fi yawa cikakkiyar martabar siyasa da ikon gudanarwa, tare da amsa tsoffin bukatu na samun wakilci kai tsaye a mulki.

Haka kuma, Jihar Neja an kirkire ta ne daga tsohuwar Jihar Arewa maso Yamma (North-Western State), matakin da ya kusantar da gwamnati ga al’ummomin da ke warwatse a daya daga cikin yankuna mafi girma a kasar.

Jihohin Ogun da Ondo an fitar da su ne daga tsohuwar Jihar Yamma (Western State), wani yanki da tun a tarihi ya shahara da tsananin neman kirkirar jihohi, sakamakon damuwa kan daidaiton cikin gida, fifikon ci gaba da kuma wakilcin siyasa.

Jihar Imo kuma ta fito ne daga Jihar Gabas ta Tsakiya (East Central State), domin magance korafe-korafen kananan kabilu a tsohuwar Yankin Gabas, tare da shimfida tubalin sake fasalin tsarin gudanarwa a yankin Kudu maso Gabas.

Shekaru 50 kenan da kirkirar jihohin bakwai, kuma sun samu gagarumin fadada ta fuskar yawan jama’a, ababen more rayuwa da kuma muhimmancin siyasa. Wasu daga cikinsu ma an sake rarraba su a cikin karin kirkirar jihohi da aka yi daga baya, lamarin da ke kara nuna muhimmancin tunanin Murtala Mohammed na rarraba iko.

An kirkiri Jihar Gombe daga Bauchi a shekarar 1996; Jihar Yobe ta fito daga Borno a 1991; Jihar Abia an fitar da ita daga wani bangare na tsohuwar Imo a 1991; Jihar Ekiti an kirkire ta daga Ondo a 1996. Sai dai Binuwe, Neja da Ogun sun ci gaba da kasancewa cikin iyakokinsu na asali tun daga shekarar 1976.

Haka kuma, a cikin shekaru hamsin da suka gabata, jihohin bakwai sun samar da shugabanni a manyan matakan rayuwar kasa, ciki har da gwamnonin jihohi, ministoci, manyan hafsoshin soja, ‘yan majalisa, har ma a wasu lokuta mataimakan shugaban kasa da shugabannin kasa. Sun bayar da gagarumar gudummawa ga tattalin arzikin Nijeriya ta fannoni kamar noma, masana’antu, makamashi, kasuwanci da bunkasa jarin dan’Adam.

Jihar Ogun ta fito a matsayin cibiyar manyan masana’antu; Jihar Binuwe ta ci gaba da rike martabarta a matsayin jihar da ke samar da abinci; Jihar Neja na dauke da muhimman cibiyoyin samar da wutar lantarki ta ruwa; Jihohin Borno da Bauchi na taka muhimmiyar rawa a harkokin noma da kasuwanci; Jihar Imo ta ci gaba da kasancewa cibiyar ilimi da kasuwancin kirkire-kirkire; yayin da Jihar Ondo ke bayar da gudummawa ta fannin noma, ma’adanan kasa da kuma bunkasar albarkatun dan’Adam.

Sai dai duk da muhimman nasarorin da aka samu a jihohin da abin ya shafa, masu lura da al’amura na ganin cewa bikin cikar shekaru 50 da kafuwarsu ya kuma kamata ya zama lokaci na zurfin tunani, ganin cewa da yawa daga cikin alkawurran da aka yi a lokacin kirkirar jihohin—kamar ingantaccen shugabanci, saurin bunkasa ci gaba, karin tsaro da dogaro da kai ta fuskar tattalin arziki har yanzu ba su cika yadda aka yi fata ba, ko kuma sun cika ne kadan.

Jihar Bauchi na ci gaba da fuskantar matsaloli irin su yawan talauci, karancin kudaden shiga na cikin gida (IGR) da rashin aikin yi musamman a tsakanin matasa.

Abin takaici, jihohin Bauchi da Gombe suna fama da rikici kan mallakar filin man fetur da iskar gas na Kolmani, inda kowaccensu ke ikirarin cewa rijiyoyin man na cikin yankinta. A cikin ‘yan shekarun nan, wannan takaddama ta ci gaba da bayyana.

Wurin, wanda ke dauke da Lasisi na Binciken Man Fetur (OPL) 809 da 810, wanda ya ratsa Kolmani One, Two, Three, Four da Fibe, an kaddamar da shi ne a zamanin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari. Rahotanni sun nuna cewa wurin na dauke da kusan ganga-gangan man fetur biliyan daya da kuma biliyan 500 na kafar cubic na iskar gas.

Ci gaban Jihar Binuwe ya sha wahala sakamakon rikice-rikicen manoma da makiyaya da ake yi a kai a kai, tilastawa al’ummomin karkara yin hijira, da raunin damar sarrafa amfanin gona, duk da irin damar noma da jihar ke da shi.

Abin takaici, a jiya ne Kotun Koli ta Tarayya a Abuja ta umarci a tsare wasu da ake zargin su a matsayin masu hannu a hare-haren tashin hankali da aka kai a Al’ummar Yelwata a Jihar Binuwe, inda mutum kusan 150 suka rasa rayukansu tar da lalata dukiyoyi.

Jihar Borno kuwa na ci gaba da daukar nauyin tasirin dogon lokaci na ta’addanci, matsalolin jin kai da bukatun sake gina wuraren da rikici ya shafa.

Abin takaici, bikin cikar shekara 50 da jiha ta yi ya zo ne a daidai lokacin da aka samu labari mara dadi cewa ‘yan Boko Haram sun kashe mutum 17 a Borno!

Jihar Imo na fuskantar rashin kwanciyar hankali a siyasa; kalubalen tsaro da suka danganci tashin hankali na masu neman rabuwar kai, da kuma raguwar amincewar jama’a ga gwamnati.

Jihar Neja, duk da kasancewarta mai dauke da muhimman kadarori na kasa a fannin makamashi da noma, tana fama da matsalolin ’yan fashi da makami, karancin ci gaba da kuma matsalolin muhalli, ciki har da ambaliyar ruwa da matsalolin hijirar mutane sakamakon matattarar ruwa.

Dangane da albarkatu da girma, Jihar Neja, wacce ke da kusan kilomita murabba’i 76,363, ita ce jihar mafi girma a Nijeriya ta fuskar kasa, kuma a halin yanzu ta fi kowace daga tsofaffin Yankin Yamma da Gabas girma tun lokacin samun ‘yancin kai.

Jihar na da kusan kashi 8 na yawan kasar Nijeriya baki daya, ta yi iyaka da jihohi 7 (Kaduna, Zamfara, Kebbi, Kogi, Kwara, Babban Birnin Tarayya da Nasarawa), sannan tana da iyaka ta kasa da Jamhuriyar Benin.

Jihar na dauke da manyan koguna da ruwa, ciki har da Kogin Neja, Kogin Kaduna, da matattarar ruwa Kainji, Jebba da Shiroro, wanda ke ba ta muhimmanci wajen noman rani da samar da wutar lantarki ta ruwa.

Abin takaici, duk da girma da albarkatun kasar, yawan jama’a a jihar har yanzu masu rauni ne, kuma manyan sassan jihar har yanzu karkara ne kuma ba su ci gaba ba, inda masana ke kiran su “wuraren da ba a kula da su”.

Har yanzu, Jihar Ogun na fuskantar kalubale wajen sarrafa saurin bunkasar masana’antu yayin da take fama da matsalolin ababen more rayuwa, rikicin kasa da lalacewar muhalli.

Jihar Ondo kuwa tana ci gaba da fama da raguwar amfanin gona, karancin bambance-bambancen tattalin arziki da rashin daidaiton manufofi.

Abin dariya, a lokacin da wadannan jihohin makwabta za su kasance suna bikin nasu ci gaba, Jihohin Ogun da Ondo a halin yanzu suna cikin rikici kan mallakar Tsibirin Eba, wani yanki mai arzikin mai a Kudu maso Yamma, bayan amincewar Shugaba Bola Tinubu da gudanar da aikin hako mai a rijiyar mai da aka yi watsi da ita a tsibirin.

A karshen mako, Gwamnatin Jihar Ogun ta sake tabbatar da ikonta kan Tsibirin Eba, da ke cikin Karamar Hukumar Ogun Waterside.

Haka kuma, ta yi tir da Jihar Ondo kan ikirarin mallakar wannan yanki, inda ta bayyana cewa matakin na Ondo yana tayar da husuma.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, Mataimakin Musamman na Gwamna Dapo Abiodun kan Harkokin Bayani da Dabarun Sadarwa, Kayode Akinmade, ya ce tsibirin na cikin iyakar Jihar Ogun ne bisa tarihi, doka da takardun gudanarwa.

Sai dai, Jihar Ondo ta ki amincewa da ikirarin Ogun, tana mai cewa tsibirin yana karkashin Atijere a Kramar Hukumar Ilaje.

A cikin wata sanarwa ma a ranar Lahadi, Mataimakin Musamman na Gwamna Lucky Aiyedatiwa kan Sadarwa da Dabarun Harkoki, Allen Sowore, ya zargi Ogun da bayar da bayanan jama’a da suka rikita gaskiya a kafafen yaDa labarai.

Ya ce duk da cewa ana gane jihohi da al’ummomin da suke karbar bakuncin yankuna, ikrarin mallaka na yankin dole ne a tabbatar da shi ta hanyar tarihin kasa, shaidun takardu, da hukunci na doka ko kotu.

A fadin jihohin bakwai, matsaloli iri daya na ci gaba da kasancewa, ciki har da dogaro da kudaden da gwamnati ta tarayya ke bayarwa, karancin kudaden shiga na cikin gida, rashin aikin yi a tsakanin matasa, rashin tsaro, da rashin ingantaccen shugabanci da rikon amana.

Duk da haka, ba tare da yin girman kai ba, idan marigayi Janar Murtala Mohammed zai duba jihohin bakwai da ya kafa a ranar 3 ga Fabrairu, 1976, za a iya tsammanin cewa zuciyarsa ba za ta fi son girman su ko matsayin su ba, sai dai ruhinsu. Bai kirkire su a matsayin masu yin gasa marar karewa ba, sai dai a matsayin abokan aiki a cikin wani aikin kasa na hadin kai, a matsayin sassa masu karfi da za su iya mulkansu da kansu, amma masu hikima da za su iya dogaro da juna.

Murtala da alama zai so ganin wadannan jihohi suna hade ta hanyar tarihi da manufa, yana gane cewa tarihin su, al’ummominsu da tattalin arzikinsu sun yi kakaken hadin kai. Zai ji haushi ganin yadda rigingimun siyasa, shakku na kabilanci da tunanin samun riba kawai sau da yawa suka raunana ikon hadin kai, alhali rashin tsaro, talauci, matsalolin yanayi da karancin ababen more rayuwa ke ci gaba da shafar iyakokinsu ba tare da bambanci ba.

A hangen nesansa, hadin kai ba zai kasance taimako na jin kai ba, sai dai dabara ce. Kowacce jiha na da fa’ida ta musamman, ko a fannin noma, jarin dan’Adam, kasuwanci, albarkatun kasa ko matsayi na kasa. Idan aka hada wadannan karfi, za su iya zama karfi guda mafi girma fiye da jimillarsu, ta hanyar kasuwanni masu hadin kai, tsaro daidaitacce, hanyoyin sufuri hadeddu da zuba jari na hadin gwiwa a fannin ilimi da masana’antu.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *