Kotun Birtaniya ta yanke wa ɗan Najeriya hukuncin daurin rai-da-rai kan kashe budurwarsa

[ad_1]



Wata kotu a Birtaniya ta yanke wa Adedapo Adegbola, ɗan Najeriya mai shekaru 40, hukuncin daurin rai-da-rai bisa laifin kisan tsohuwar budurwarsa kuma ɗalibar jami’a.

Kotun dai ta sami Adedapo da laifin kashe budurwar tasa mai suna Steph Irons, mai shekaru 23 a birnin Nottingham na kasar.

A cewar rahoton kafar Rahoton Irish na ranar Alhamis, kotun Nottingham Crown ta yanke masa hukunci bayan ya amsa laifin kashe Steph a gidanta da ke Mapperley a ranar 21 ga Oktoba, 2025, bayan lalacewar soyayyar su wadda ba ta daɗe ba.

An dai shaida wa kotun cewa sun haɗu ne yayin aiki tare, suka yi soyayya na ɗan lokaci kafin su rabu.

Lauyoyin gwamnati sun shaida wa kotun cewa Adedapo ya kamu da ciwon zuciya bayan rabuwarsu da ita, inda ya sayo wuƙa guda biyu ta yanar gizo sannan ya ɗauki motar haya zuwa gidanta.

Lauyoyin sun ce ya kai mata hari lokacin da ta fito waje domin zubar da shara, sannan ya shiga cikin gidan ya yi ta daba mata wuƙar.

Daga bisani ’yan sanda sun gano gawarta a falonta, inda aka tabbatar da mutuwarta a wurin.

Bayan kisan, rahotanni sun ce Adedapo ya gudu, ya jefar da kayan da jini a jikinsu da sauran shaidu a titunan Mapperley da Carlton.

Rundunar ’yan sandan Nottinghamshire ta ce ya bi ta Mansfield, Worksop, Sheffield da Hull kafin daga bisani ya mika kansa.

Alƙalin kotun ya yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai tare da sharadin zama a kurkuku na akalla shekaru 25.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *