Ba na buƙatar kundin tsarin mulki wajen bai wa shugabanni shawara — Sanusi II

[ad_1]



Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce ba ya buƙatar kundin tsarin mulki kafin ya bai wa Shugaban Ƙasa ko gwamnonin jihohi shawara.

Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a gidan talabijin na Channels a ranar Laraba.

Sanusi II, ya ce sarakunan gargajiya na da muhimmiyar rawa a tsarin mulkin Najeriya kuma suna taimakawa wajen gina ƙasa.

Ya ƙara da cewa ikon ba da shawara yana fitowa ne daga jama’ar da yake jagoranta, ba daga doka ba.

“Shin dole ne faɗa wa Shugaban Ƙasa shawara? Idan na ga wani abu ba daidai ba a ƙasar nan, zan je wajdn Shugaban Ƙasa n faɗa masa.

“Ba na buƙatar kundin tsarin mulki ya faɗa min abin da zan faɗa wa gwamna. Ina da wannan iko ne saboda ni jagoran al’umma ne,” in ji shi.

Sarkin, ya kuma yi kira da a ƙara bai wa mata dama a siyasa, yana mai cewa ba za a iya samun ci gaban ƙasa ba tare da rawar da mata ke takawa ba.

Haka kuma ya yi Allah-wadai da cin zarafin mata da ake yi, yana cewa al’ada ba za ta iya zama hujja wajen aikata hakan ba.

“Ba za ka iya dukan mace ba saboda al’adarka ta yadda da hakan ba. Ita ’yar ƙasa ce kuma tana da haƙƙin samun kariya,” in ji shi.

Sanusi ya shahara wajen faɗin albarkacin bakinsa tun lokacin da yake Gwamnan Babban Bankin Najeriya daga 2009 zuwa 2014.

A baya ya riƙa sukar cin hanci da aikata rashin gaskiya.

Tun bayan hawansa sarautar Kano, ya ci gaba da magana kan talauci, ilimi, rashin tsaro da gazawar shugabanci.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *