Kotu Ta Yanke Wa Ɗan Fashi Hukuncin Kisa A Nasarawa


Babbar Kotun Jihar Nasarawa ta yanke wa Saidu Idi hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe Hardo Adamu Buli yayin wani fashi da makami da ya faru a shekarar 2015.

Babbar Mai Shari’a ta jihar, Justice Aisha Mohammed Usman, ta same shi da laifin fashi da makami da kuma kisan kai.

  • Fadin Filaye Masu Dausayi Na Sin Ya Kai Matsayi Na Hudu A Duniya
  • An Fitar Da Sakon Bidiyo Na Yayata Shirye-Shiryen Bikin Bazara Na CMG A Afirka Ta Kudu

Babban Lauyan Jihar Nasarawa kuma Kwamishinan Shari’a, Isaac Danladi, ya ce kotu ta wanke Saidu Idi daga laifin haɗa baki, amma ta same shi da laifi a kan sauran tuhume-tuhumen.

Ya bayyana cewa an harbi mamacin a ciki kafin a ƙwace masa kuɗi da sauran kayayyaki.

Kotu ta ce ɓangaren masu gabatar da ƙara sun tabbatar da laifin wanda ake tuhuma ba tare da wata shakka ba.

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta ce hukuncin ya nuna cewa ba za a yadda da aikata laifi ba, tare da gargaɗin cewa duk masu aikata fashi da makami za su fuskanci hukunci.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *