Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Bindiga Da Dama A Sansanin Gwaska Ɗanƙarmi A Jihar Zamfara


Dakarun Rundunar Sojin Nijeriya sun kashe ’yan bindiga da dama a wani gagarumin samame da suka kai kan sansanin shahararren shugaban ’yan bindiga, Gwaska Dan Karmi, da ke karamar hukumar Maru a Jihar Zamfara. Rundunar ta ce harin hadin gwiwa ne na kasa da sama, bayan samun sahihan bayanan sirri.

Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Soji ta 8 Division, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi. Ya ce dakarun karkashin Sashe na 2 na Operation FANSAN YAMMA ne suka gudanar da aikin.

  • Tsaro: An Sake Buɗe Kwalejin Jihar Kwara Bayan Rufeta A Baya
  • Wang Yi Ya Tattauna Da Sakataren Hukumar Tsaro Ta Rasha

Osoba ya ce bayanai sun nuna cewa ’yan bindiga fiye da 100 sun hallara a sansanin domin shirya manyan hare-hare kan al’ummomin da ke kusa da kuma wuraren kayan agajin soji. Bayan sa ido na kwanaki a asirce, dakarun sojin kasa tare da goyon bayan Rundunar Sojin Sama (NAF) suka kai farmaki a ranar 31 ga Janairu, lamarin da ya haddasa musayar wuta.

Ya kara da cewa ’yan bindigar sun yi kokarin kewaye sojojin, amma anyi amfani da karfin makamai da dabarun soji aka fatattake su. An kashe da dama daga cikinsu, yayin da wasu suka tsere dauke da raunukan harbin bindiga. Daga bisani, an kona sansanin kafin sojojin su janye.

Osoba ya ce Rundunar Sojin Sama na ci gaba da kai hare-haren tsare hanya domin kama ’yan bindigar da suka gudu, yayin da dakarun kasa ke ci gaba da mamaye yankin domin hana su sake taruwa. Ya jaddada cewa sojoji za su ci gaba da kai hare-hare domin murkushe ’yan bindiga a fadin yankin Arewa maso Yamma.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *