Sheikh Khalifa Usman Kusfa Rigi-rigi ya rasu
[ad_1]
Allah ya yi wa shahararren malamin Musulunci, Sheikh Khalifa Usman Idris Kusfa, rasuwa bayan fama da doguwar jinya.
Surikin malamin, Malama Abubakar Ɗanyaro ya tabbatar wa Aminiya cewa Sheikh Khalifa Usman Kusfa wanda aka fi sani da Rigi-Rigi ya rasu ne a asibiti a daren ranar Lahadi a Kaduna.
Abubakar Ɗanyaro ya bayyana cewa sa ran gudanar da Sallar Jana’izarsa a yau Litinin bayan Sallar La’adasar a gidansa da ke unguwar Kusfa a Zariya, bisa koyarwar addinin Islama.
Ya shaida wa wakilinmu cewa Sheikh Rigi-Rigi ya yi fama da rashin lafiya tsawon lokaci, inda aka kwantar da shi a Asibiti Sojoji na 44 da ke Kaduna.
Daga baya aka mayar da shi wani asibiti mai zaman kansa a unguwar Barnawa Kaduna inda a nan Allah Ya karɓi rayuwarsa da misalin ƙarfe uku da rabi na dare.
Abubakar Ɗan Yaro yace za a gudanar da jana’izar marigayin a yau Litinin da misalin karfe 4:30 da rabi ɓayan sallar La’asar
Sheikh Rigi-Rigi ya yi fice da salon wa’azinsa, musamman wajen bayyana ƙaramomin waliyyai da manyan malamai.
A baya-bayan nan, bidiyon Sheikh Rigi-Rigi da wa’azinsa sun riƙa ɗaukar hankali musamman a kafofin sada zumunta, inda yake koyarwa kan ƙaramomin waliyyai da almajiran Sheikh Ibrahim Inyass waɗanda ba kasafai ake jin sunayensu ba, kuma sunayen nasu na da maya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link