Sin Ta Nuna Matukar Adawa Da Hana Al’ummar Cuba ‘Yancin Rayuwa Da Samun Ci Gaba

[ad_1]

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, a yau Jumma’a ya bayyana matukar adawar kasar da matakai da ayyukan da ba su dace ba da ka iya hana al’ummar Cuba ‘yancinsu na rayuwa da samun ci gaba.

Mai magana da yawun ma’aikatar Guo Jiakun ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake bayar da amsar tambayar da aka yi game da wani umarni na bangaren zartarwa da shugaban Amurka Donald Trump ya sanya wa hannu a jiya Alhamis, wanda ke barazanar kakaba karin haraji kan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen da suke samar da mai ga Cuba.

A yayin taron manema labaru na yau da kullum, Guo ya ce, “Kasar Sin tana goyon bayan Cuba sosai wajen kare ‘yancinta na kasa da tsaronta, kana tana yin fatali da tsoma baki daga waje.” (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *