Sin: Ra’ayin Nuna Karfin Soji Zai Jefa Gabas Ta Tsakiya Cikin Mawuyacin Hali

[ad_1]

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya gabatar da jawabi a budaddiyar muhawarar da kwamitin sulhu na MDD ya gudanar a jiya Laraba kan batun Gabas ta Tsakiya, inda ya ce, karfin soja ba zai iya warware matsaloli ba, kuma duk wani matakin soja ba abun da zai haifar sai jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin mawuyacin hali, irin wanda ba a taba gani ba.

Fu Cong ya ce, Iran kasa ce mai cin gashin kanta dake da cikakken ikon mulki, kuma al’ummar Iran ne kadai ke da ’yancin yanke shawara kan al’amuran kasarsu. Kazalika, bangaren kasar Sin yana goyon bayan kokarin da Iran ke yi na tabbatar da kwanciyar hankalin kasa, da goyon bayan kare ikon mulki, da tsaro da cikakkun yankunanta.

Ya ce, bangaren Sin yana kira ga dukkan bangarori da su yi biyayya ga manufa, da ka’idojin kundin mulkin MDD, yana kuma nuna adawa da tsoma baki cikin al’amuran cikin gidan wasu kasashe, da kuma adawa da amfani da karfin soja, ko yin barazanar amfani da shi a dangantakar kasa da kasa.

Har ila yau, bangaren Sin yana fatan Amurka da sauran bangarori masu alaka da batun, za su yi la’akari da kiran al’ummun kasa da kasa da kasashen yankin, wajen aiwatar da matakai da suka dace don shimfida zaman lafiya, da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya, ta yadda za a guje wa tayar da hankali da karuwar hargitsi.

Fu Cong ya kara da cewa, bangaren Sin yana fatan hadin gwiwa tare da al’ummun kasa da kasa, wajen mutunta zabin al’ummar Gabas ta Tsakiya na cin gashin kansu, da kula da abubuwan da suke damuwar kasashen yankin, tare da taka rawar gani wajen shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *