Tawagar Jami’an Lafiya Ta Sin Ta Gudanar Da Aikin Duba Lafiyar Marayu Kyauta A Zanzibar
[ad_1]
Tawaga ta 35 ta jami’an lafiyar kasar Sin dake aiki a kasar Tanzaniya, ta gudanar da aikin duba lafiyar marayu kyauta a tsibirin Zanzibar na kasar, karkashin wani shiri mai lakabin “Tawagogin jami’an lafiya 100 a kauyuka 1,000”.
Tawagar likitocin ta gudanar da aikin ne a ranar Lahadi, inda jami’anta suka duba lafiyar yara kimanin 70 a fannoni takwas, ciki har da na magance cututtuka, da aikin tiyata, da magungunan gargajiyar kasar Sin.
Domin biyan bukatun kiwon lafiya na marayun, tawagar ta shirya wani taro na ilmantarwa game da matakan kiwon lafiya. Tawagar ta gabatar da takardu masu dauke da bayanai ta amfani da harshen Swahili, inda suka horar da yaran dabarun kandagarkin cututtuka, da na tsafta, da wanke hannu da na kula da hakora. Bayan kammala horon, tawagar ta raba muhimman kayayyaki ga yaran, ciki har da magunguna, da kayan masarufi da na karatu da abinci.
Da yake tsokaci kan wannan aiki, jagoran tawagar jami’an lafiyar Bao Zengtao, ya ce yara su ne makomar kawancen Sin da Afirka, kuma tawagar na da nufin ingiza musaya mai zurfi, da hadin gwiwa ta hanyar amsa kira game da shekarar musayar jama’a ta Sin da Afirka ta shekarar 2026. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link