Shugaban Hukumar Alhazai da ƙarin kwamishinoni biyu sun yi murabus a Kano
[ad_1]
Wasu manyan jami’an Gwamnatin Kano uku sun yi murabus daga muƙamansu, bisa abin da suka bayyana a matsayin sauye-sauyen siyasa da buƙatar sake daidaita alƙiblarsu.
Aminiya ta ruwaito cewa waɗanda suka ajiye aikin sun haɗa da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Ayyuka na Musamman, Air Vice Marshal Ibrahim Umaru (mai ritaya), Kwamishinan Ayyuka na Musamman, Nasiru Sule Garo, da kuma Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabiu.
AVM Ibrahim Umaru ya sanar da murabus ɗinsa ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa Gwamna Abba Kabir Yusuf ta hannun Sakataren Gwamnatin Jihar, mai ɗauke da kwanan wata 26 ga Janairu, 2026.
A wasiƙar, Umaru ya gode wa gwamnan bisa amanar da ya ba shi, yana mai tunatar da cewa tun farko an naɗa shi Darakta Janar na Hukumar Ayyuka na Musamman a watan Yunin 2023, kafin daga bisani a ɗaga likafarsa zuwa muƙamin kwamishina.
Ya ce, “Babban alfahari ne a gare ni da aka ɗora mini nauyin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Kano a ƙarƙashin jagorancinku.”
AVM Umaru ya bayyana cewa murabus ɗinsa ya biyo bayan wasu sauye-sauyen siyasa na baya-bayan nan, inda ya ce ya ɗauki matakin ne domin amfanin jihar da gwamnatin baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa, ya yi aiki ne bisa ƙa’idojin tafiyar Kwankwasiyya ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wadda ta ke mayar da hankali kan adalci, ɗa’a da yi wa jama’a hidima.
Shi ma Kwamishinan Ayyuka na Musamman, Nasiru Sule Garo, ya sanar da murabus ɗinsa cikin wata wasiƙa da ya aike wa gwamnan a ranar 26 ga Janairu, yana mai cewa ya ɗauki matakin ne bayan dogon nazari.
Garo ya ce hidimta wa al’ummar Kano babbar girmamawa ce a gare shi, yana kuma tabbatar da cewa zai taimaka wajen miƙa aiki yadda ya kamata domin sauƙaƙa sauyin mulki.
A gefe guda kuma, Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabiu, shi ma ya sanar da murabus ɗinsa yana mai alaƙanta matakin da sauye-sauyen siyasa da kuma buƙatar sake daidaita alkiblarsa.
Rabiu ya ce murabus ɗinsa ya dogara ne kacokam kan biyayyar da yake yi wa tafiyarsu ta Kwankwasiyya da shugabanta, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yana mai cewa matakin zai ba shi damar bayar da cikakken gudunmawa wajen cimma manufofin tafiyar a wannan lokaci.
Ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da aka ba shi na jagorantar hukumar, tare da yaba wa ma’aikata da ‘yan kwamitin hukumar kan haɗin kai da goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake kan muƙamin.
Tuni dai shi ma ɗan Kwankwaso, Kwamishinan Matasa da Wasanni na Kano, Mustapha Rabiu Kwakwaso ya sanar da ajiye muƙaminsa, lamarin da ya zuwa yanzu kwamishinoni uku sun yi hannun riga da aiki a ƙarƙashin gwamnatin Abba Kabir Yusuf.
Aminiya ta ruwaito cewa, a wannan Litinin din ce Gwamna Abba Kabir ya koma jam’iyyar APC, bayan da aka shafe makonni ana dakon shigarsa, lamarin da ya sa fagen siyasar Jihar Kano ya ɗauki ɗumi, musamman bayan fahimtar ɓaraka tsakaninsa da ubangidansa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link