An Yi Bikin Murnar Kaddamar Da Shekarar Musayar Al’adu Da Cudanyar Jama’a Ta Sin Da Afirka Ta Mauritius
Kwanan baya, an gudanar da bikin bude jerin aikace-aikace domin murnar kaddamar da shekarar musayar al’adu da cudanyar jama’a ta Sin da Afirka ta kasar Mauritius, wato murnar bikin bazara ta shekarar 2026, a cibiyar al’adun kasar Sin ta Mauritius dake birnin Port Louis, fadar mulkin kasar Mauritius.
Jakadar kasar Sin dake kasar Mauritius Huang Shifang, ta gabatar da jawabin cewa, matasa su ne makomar dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka, kana fasahar AI tana yin muhimmin tasiri ga bunkasar zaman takewar al’ummar kasashen duniya, don haka ne ma aka kaddamar da shekarar musayar al’adu da cudanyar jama’ar Sin da Afirka, wato jerin shirye-shiryen murnar bikin bazara, da gasar fasahohin AI ta matasa, mai taken “Zumuncin Sin da Afirka”, domin inganta cudanyar jama’ar Sin da Afirka da samun makoma mai haske.
Haka kuma, cikin jawabinta, shugabar kwalejin tsarawa da yin kirkire-kirkire ta kasar Mauritius, ta bayyana cewa, gasar fasahohin AI ta matasa mai taken “Zumincin Sin da Afirka”, wata gasa ce ta nuna ra’ayoyin yin kirkire-kirkire ta fasahar AI, da taya murnar zurfafa zumuncin dake tsakanin kasashen biyu, tare da inganta cudanyar jama’a a tsakanin juna. Mahalarta wannan gasa za su yi amfahi da fasahar AI wajen gudanar da aikinsu, inda za su nuna kyakkyawan zumunci, da makomar hadin gwiwar Sin da Mauritius ta hanyar hada kimiyya da fasaha cikin ayyukan fasahar su. (Mai Fassara: Maryam Yang)