Osimhen Ya Zura Ƙwallonsa Ta 50 A Galatasaray
[ad_1]
Ɗan wasan gaban ƙungiyar Super Eagles ta Nijeriya, Victor Osimhen, ya cimma wata babbar nasara bayan da ya zura kwallonsa ta 50 tun bayan komawarsa ƙungiyar Galatasaray ta ƙasar Turkiyya, a wasan da suka doke Fatih Karagumruk a gasar Super Lig a daren Asabar a filin wasa na Atatürk Olimpiyat.
Wasan ya fara da sauri, inda Gabriel Sara na Galatasaray ya jefa ƙwallo a ragar Karagumruk tun a minti na farko. Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Sara ya ƙara wa ƙungiyar tasa ƙwallo ta biyu, yana ƙara matsa lamba kan abokan hamayya.
A minti na 55 ne Victor Osimhen ya zura tasa, wadda ta zama ƙwallo ta 50 da ya ci wa babbar ƙungiyar da ke birnin Istanbul, abin da ya ƙara tabbatar da muhimmancinsa a cikin tawagar.
A wannan kakar wasa, Osimhen ya riga ya zura ƙwallaye bakwai a gasar Super Lig, tare da wasu 13 a sauran gasa da ya buga. Nasarar da Galatasaray ta samu ta tabbatar da kasancewarta a saman teburin gasar da tazarar maki huɗu tsakaninta da Fenerbahce da ke matsayi na biyu.
[ad_2]
Source link