Ƙwace Mulki A Hannun Tinubu Ne Kaɗai Hanyar Ceto Nijeriya A 2027 — ADC

[ad_1]

Jam’iyyar haɗaka ta ADC ta bayyana cewa ƙwace mulki a hannun Shugaba ƙasa Bola Tinubu ne kaɗai hanyar ceto Nijeriya daga abin da ta bayyana a matsayin mummunan rikicin shugabancin ba a tava ganin irinsa ba.

Mai magana da yawun jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya bayyana hakan a ranar Juma’a a yayin wata hira a shirin siyasa na gidan talaijin na Channels, inda ya musanta cewa ba za a iya ceto ƙasar nan ba idan har wannan gwamnati tana kan mulki.

“Wannan shi ne a ajendar, amma ba shi ne ra’ayoyin ƴan Nijeriya gaba ɗaya ba. Sai da kuma babu yadda za a yi Tinubu na kan mulki a iya ceto Nijeriya.

“A duk lokacin da mutane ke cewa za ka iya ɗaukewa da gudu da wani muhimmin abu ba tare da la’akari da yin tunani ba, tabbas wannan kalamun ƴan bindiga ne,” in ji Abdullahi.

  • Atiku Ne Ya Fi Dacewa Da Tikitin Takara A ADC Amma Ya Kamata Ya Janye — Baba-Ahmed
  • Atiku Ya Yi Murna, Ya Yi Marhaba Da Peter Obi A ADC

Haka kuma Abdullahi ya nuna damuwarsa game da zargin da ake yi wa ƴan majalisa na sauya dokar haraji wanda aka ƙaƙaba wa ƴan Nijeriya a wannan shekara, ya sava wa dimokuraɗyyar ƙasar nan.

Ya zargi gwamnati da aiwatar da wasu ƙudirorin na ƙasashen ƙetare waɗanda ba su dace da tsarin mulkin ƙasar nan ba.

“Gwamnatin da za ta iya amicewa da dokar da aka yi wa cushe, me kake kiran irin wannan gwamnati?” ya tambaya.

Ya musanta cewa a cikin kasafin kuɗin 2026, yawan kuɗaɗen da za a kashe a wasu abubuwa marasa fifiko ya nuna cewa gwamnatin ta gaza. Ya ce saka irin wannan adadin a vangaren tsaro na cikin gida zai ba da sakamako mafi kyau fiye da ƙoƙarin tabbatar wa shugabannin ƙasashen waje cewa Nijeriya tana zaune lafiya.

“Ba su damu da yadda ‘yan Nijeriya ke ci gaba da mutuwa. Ba su damu cewa mutane na ci gaba da hallaka ba. Abin da suke so kawai shi ne, su sami fada a gaban Amurkawa,” in ji Abdullahi.

Mai magana da yawun ADC ya nuna damuwa kan yarjejeniyar fahimtar juna ta likitanci tsakanin Nijeriya da Amurka, wadda aka ruwaito an sanya hannu a kanta a ranar 19 ga Disamba, wanda ya yi iƙirarin cewa za ta bai wa Amurka ikon sarrafawa da rarraba kuɗaɗe sosai duk da cewa Nijeriya ce ke bayar da mafi girman gudummawar kuɗi.

“Babu ɗan Nijeriya da ya ga cikakkun bayanan wannan yarjejeiya” in ji shi, yana bayyana sharuɗɗan a matsayin abin mamaki yayin da ya yi tambayoyi game da ikon mallaka na ƙasa da ƙasa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *