Gyaran Amarya Kafin Lokacin Aure

[ad_1]

Iyayanmu mata ya kamata musan cewa duk lokacin da za a yi auren ƴarmu ya kamata ki san cewa akwai wasu abubuwa da za mu gyara jikin ƴarmu, ba wai haka za ki ɗauki ƴarki ki miƙata gidan miji ba babu gyara babu komai ko budurwa ce ita ma aka fi so a gyara.

Nana Aisha Allah ya ƙara mata yarda take cewa lokacin da na kusa tarewa a kai ni gidan mazon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam), kun san lokacin da aka yi aurenta tana ƙarama lokacin da za ta tare ba ta da jiki ba ta da ƙiba tana siririya, sai ga Nana Aisha ta ce ana haɗa abubuwa guda biyu ana bata tana amfani da su kuma cikin yardar Allah kafin a kaita sai da ta yi bulbul ta yi kyau kuma ta yi haske.

  • ‘Yansanda Sun Kama Amarya Kan Zargin Kashe Mijinta Da Guba A Jigawa
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Amarya Da Baƙin Biki A Sokoto

Waɗannan abubuwan guda biyu ya kamata mu ma iyaye mu yi wa ƴa’yanmu amfani da su kafin mu kai su gidan miji. Na farko akwai Kokumba, sannan akwai ɗanyan dabino.

Yadda ake amfani da su shi ne:

Za ki samu Kokumba kamar guda ɗaya sai ki raba ta uku, ki ɗauki ɗaya daga ciki sai ki wanke ta ki yayyanka ta, da safe, bayan amarya ta gama cin abinci sai ki ba ta ta ci tare da ɗanyen dabino, idan da hali za ki iya ba ta sau biyu a rana kamar safe da dare, ita Kokumbar nan idan kika raba ta uku kin ga ta yini ɗaya ce da ta washegari da safe, Dabino shi kuma kamar biyu ko uku ma ya isa idan ta ci kashi ɗayan Kokumba sai ta ci ɗanyen Dabino biyu ko uku haka za tai ta yi har zuwa lokacin bikin.

Ana fara ba wa amarya waɗannan ɗanyan kayan kamar wata uku ko biyu ko wata ɗaya ma idan hakan bai samu ba kafin lokacin aure. Jikinta ta zaiyi kyau za tayi bulbul fatarta ma za tayi kyau da yardar Allah.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *