Xi Jinping Ya Hira Da Shugaban Brazil Luiz Inacio Lula Da Silva Ta Wayar Tarho

[ad_1]

A safiyar yau 23 ga watan Janairu, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya hira da shugaban Brazil Luiz Inácio Lula da Silva ta wayar tarho.

Shugaba Xi ya bayyana cewa, bana nan shi ne shekara ta farko na shirin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al‘ummar Sin na shakaru biyar-biyar karo na 15. Bangaren Sin zai inganta ci gaba mai inganci ta hanyar bude kasuwarta mai zurfi, yana ba da karin damammaki ga hadin gwiwar Sin da Brazil. Bangaren Sin yana son yin kokari tare da bangaren Brazil don habaka hadin gwiwa masu fa‘ida a kowane fanni, ta yadda za a kai ga dangantakar Sin da Brazil zuwa mafi samun ci gaba, da kuma makoma mai kyau.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, Sin da Brazil a matsayin muhimman mambobi na kasashe masu tasowa, su ne ingantaccin karfi mai gina zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya, da kyautata tsarin shugabancin duniya. Ya kamata su tsaya tsayin daka kan gaskiyar tarihi, don kare muradun gama gari na kasashen biyu da na kasashe masu tasowa, tare da kiyaye matsayin MDD da kuma adalcin kasa da kasa.

A nasa bangaren, Lula ya bayyana cewa, ziyarar shugaba Xi a Brazil a shekara ta 2024, ta daukaka dangantakar Brazil da Sin zuwa sabon mataki na gina duniya mafi adalci da makomar bil Adam ta bai daya mai dorewa cikin hadin gwiwa. Kuma sun samun ci gaba mai armashi a hadin gwiwarsu a fannoni daban-daban. Bangaren Brazil yana fatan kara hadin gwiwa da bangaren Sin don inganta dangantakar kasashen biyu da kuma ta Latin Amurka da Sin.(Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *