An kashe wasu a rikici tsakanin Boko Haram da ISWAP




A wani rikici da ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyin tada ƙayar baya Boko Haram da ISWAP, inda aka kashe mayaƙa da dama a ɓangarorin a ranar Talata, a ɓangaren Bukura da masu biyayya ga Abu Umaima a gefen tafkin Chadi na yankin ƙaramar hukumar Abadam a Borno.

Majiyoyin tsaro sun shaida cewa, rikicin ya ɓarke ​​ne tsakanin ƙarfe 6:00 na safe zuwa 10:15 na safen a kusa da ƙauyen Dogon Chiku Buhari, wani yanki na kan iyaka a ƙaramar hukumar Abadam, mai nisan kilomita ɓaya daga kan iyakar Najeriya da Nijar.

Majiyoyin sun ce, mayaƙan ƙungiyar Bukura, wadanda ake kyautata zaton suna aiki daga matsugunan da ke kewaye da tafkin Chad a gefen Jamhuriyar Nijar, sun yi arangama da ‘yan ISWAP mazauna yankin kan iyakar Najeriya.

“Yaƙin ya faru ne a kusa da Dogon Chiku Buhari, gabashin Tubum Mota da kuma yankin Bosso-Diffa a Jamhuriyar Nijar yadda aka dauki sa’o’i da dama kuma ya haifar da asarar rayuka masu yawa a ɓangarorin biyu,” in ji wata majiya.

Qauyen Tubum Mota, yana gabashin Malam Fatori, kimanin kilomita 19 daga garin, wanda ya kasance wurin da ƙungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi masu adawa da juna ke fuskantar barazana.

Rikicin da ya sake ɓarkewa ya samo asali ne daga dogon rikici a cikin yanayin jihadi yadda ISWAP ta yi ƙoƙarin ƙarfafa iko a fadin yankin ta hanyar daukar ko kawar da ƙungiyoyin da suka ɓalle, yayin da ɓangaren Bukura suka ƙi amincewa da yin biyayya.

Yanayin kan iyaka mai rauni yana bawa mayaƙa damar sauya sansanoninsu cikin sauri, wanda hakan ke kawo cikas ga ayyukan yaƙi da ta’addanci da sojojin Najeriya da na rundunar hadin gwiwar MNJTF ke yi.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *