“Ba Neman Kuɗi Nake Yi Ba, Na Shiga Siyasa Ne Don Ceto Al’umma” – Tsohon Shugaban DSS
[ad_1]
Tsohon Darakta-Janar na Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), Lawal Daura, ya bayyana cewa ba don neman riba ko kuɗi ya shiga siyasa ba, sai domin ceton rayuka da kuma kuɓutar da jihar Katsina daga matsalar rashin tsaro da ke addabarta. Daura ya yi wannan bayani ne a ranar Alhamis yayin taron sake haɗuwar Ƙungiyar Tsofaffin Ɗaliban Government College Funtua (FOBA), ajin 1969, inda ya samu goyon baya a kan burinsa na tsayawa takarar gwamna a zaɓen 2027.
Tsohon shugaban DSS ɗin ya bayyana kansa a matsayin “makanikin siyasa,” yana mai cewa shigarsa siyasa na nufin gyara matsalolin tsaro da suka addabi jihar. Ya ce, “Duk lokacin da ka ga makanike to da kayan aikinsa, ka san akwai matsala. Haƙiƙa, akwai matsala a jiharmu, kuma wannan na shafar mu duka.” Ya ƙara da cewa tsaro shi ne mabuɗin warware sauran matsaloli, domin idan ba a samu tsaro ba, ba za a iya magance sauran ƙalubale ba.
- Shugabannin Ƙasashe Huɗu Da Amurka Ta Kama Amurka Ta Gurfanar Da shugaban Ɓenezuela Nicolas Maduro
- DSS Ta Kama Wani Matashi Da Ya Yi Kira A Yi Juyin Mulki A Kafofin Sada Zumunta
Daura ya yi kukan cewa kasuwanni da dama a jihar da a da suke aiki har da daddare, yanzu ba sa aiki ko da a rana saboda rashin tsaro. Ya ce noma, wanda shi ne ginshiƙin tattalin arziƙin Katsina da makwabtan jihohi, ya samu babban koma baya sakamakon hare-haren masu tayar da ƙayar baya. Ya jaddada cewa ba shugabanci ko mukami ne burinsa ba, domin matsayin da ya taɓa riƙewa ya fi na gwamna girma, kuma sunansa ya riga ya yi fice har a wajen Nijeriya
A nasa ɓangaren, Shugaban FOBA, Dakta Aliyu Yahaya, ya ce ƙwarewar Daura a fannin tsaro na ba shi damar magance matsalar rashin tsaro cikin ƙanƙanin lokaci idan aka zaɓe shi. Yahaya ya kuma yi alƙawarin cewa kowane mamba na ƙungiyar zai samar masa da ɗaruruwan ƙuri’u idan ya samu tikitin tsayawa takara a ƙarƙashin kowace jam’iyyar siyasa.
[ad_2]
Source link