Xi Ya Taya Shugaban Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya Murnar Sake Lashe Zabe
[ad_1]
A yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya Faustin-Archange Touadera murna bisa sake lashe zabe a matsayin shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
A cikin sakonsa, Xi ya yi nuni da cewa, a cikin ‘yan shekarun nan, kasar Sin da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na ci gaba da zurfafa amincewa da juna a siyasance.
Ya kara da cewa, bangarorin biyu sun kuma nuna goyon baya ga junansu kan batutuwan da suka shafi muhimman muradunsu da kuma manyan abubuwa da ke ci musu tuwo a kwarya, tare da ci gaba da karfafa mu’amala da hadin gwiwa a fannoni daban-daban.
Xi ya ce yana ba da muhimmanci sosai ga kyautata alakar Sin da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Ya bayyana kudurinsa na yin aiki tare da shugaba Touadera don aiwatar da sakamakon taron kolin Beijing na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, da kuma ci gaba da inganta dangantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu, ta yadda za a samar da karin alfanu ga al’ummomin kasashen. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link