Aikin Sarrafa Iskar Gas Na Ƙasar China Ya Dakatar Da Damar Nijeriya Na Fitar Da LNG
[ad_1]
Ana hasashen cewa, Iskar Gas, samfarin LNG da Nijeriya ke fitarwa, zuwa ƙasar China, zai ragu a shekarar 2026.
Wannan dai, na zuwa ne, bayan da ƙasar ta China, ke sa burin ƙaddamar da wani gagarumin aiki na cikin gida, na ƙara bunƙasa sarrafa Iskar Gas ɗin.
Kasancewar ƙasar kan gaba wajen sayen Iskar Gas ɗin da kuma fitar da shi, buƙatarsa, na ƙara ƙaruwa, wanda hakan ya sanya, dole ne, ƙasar, ta sauya hasashen na ta.
- Yadda Takaddama Ta Kaure Bayan Ceto Daliban Neja 130
- Kakakin Babban Yankin Sin: Jawabin Jagoran Taiwan Lai Ching-Te Cike Yake Da Karairayi Da Nuna Kiyayya
Ƙasar ta China dai, kusan ƙasa da shekaru goma da suka gabata, ta na ta haƙilon ganin ta kafa ta ta, masana’antar ta sarrafa Iskar Gas, ɗin samfarin LNG, musamman a yankin sahara.
Tsarin ƙasar ta China na yin amfani da sahara, ya sha da ban da na ƙasar Amurka, inda hakan kuma ke bai wa wasu kamfanini matsala, wajen samun sarrafa shi, domin gudanar da kasuwanci.
A yanzu, dai ƙasar ta China, ta ksance ɗaya kan gaba wajen samar da Mai da kuma Gas, fiye da a baya, musamman ganin yadda a yanzu. Ta sanar da yin amfani da yankin sahara, domin sarrafa Gas ɗin.
Bisa wasu alƙaluma na rahoton da Kpler ya fitar a cikin watan Janairun 2026, hakan ya nuna cewa, a watan Nuwambar shekarar 2025, ƙasar ta China ta samar da tan biliyan 22.1 wanda ya kai ƙarin kaso 7.1, a cikin ɗari, a shekarar ta 2025.
Hakazalika, wani rahoto ya nuna cewa, yawan Iskar Gas samfarin LNG da ƙasar ta China ta shagar cikin ƙasar ta daga Nijeriya, na da matuƙar yawan gaske, musamman ganin cewa, Chian, ta amince ta shigo da shi cikin ƙasar ta daga cikin ƙasar nan, musamman ta hanyar yin amfani da matatar mai ta NNPC.
[ad_2]
Source link