Yadda Kuɗin Hidimar Makarantar Yara Ke Ci Gaba Da Ci Wa Iyaye Tuwo A Ƙwarya

[ad_1]

Yanzu dai ba wani sabon labari bane ƴan makaranta sun dawo daga hutun Kirsimati da sabuwar shekara inda suka fara karatun zangon karatu na biyu, irin haka ne ya sa wasu iyalai shiga cikin halin da basu shirya shigar shi ba.Wasu iyayen kamar yadda aka samu bayani jininsu ya hau, wasu kuma basu iya yin bacci ba,daga wannan damuwa sai waccan, yayin da wasu suke ta lallashin masu gidajen da suke haya saboda kuwa lokacin da za su sake ba da kuɗin haya ya yi, wasu kuma sauran kaɗan ya rage amma basu biya ba.

Kai lamarin koda ma ace waɗanda suka shirya ma shi ne, suna fuskantar matsala, domin shiga zangon karatu na biyu ba ana maganar kuɗin makaranta kaɗai ba, akwai abubuwan da za’a saya daban daban da zarar an dawo daga hutu, wannan abin kuma ya shafi duk Iyaye ne,da waɗanda ke ɗaukar nauyin karatun wasu a faɗin Nijeriya.

  • Komawa Makarantu: Iyaye Sun Shawarci Gwamnati Kan Tsaron Ɗalibai Da Malamai
  • Ɓangaren Ilimi Ya Samu Rinjaye A Kasafin ₦985.9bn Na 2026 Da Gwamna Sani Ya Sanya Wa Hannu

Wani abin sha’awa, yayin da wasu iyayen suka iya goge kayan makarantar ƴaƴansu da kuma gyara jaka ko sayen wata,wasu ƴaƴansu ba za su koma makaranta da wuri ba, sai wasu sun jira an yi albashi watan Janairu tukuna.

Binciken da LEADERSHIP Lahadi tayi ya nuna yawancin makarantu masu zaman kansu suna buyƙatar a basu kashi 50 na kuɗin makaranta, kafin abar su ƴan makaranatar su shiga cikin ta. su fara harkokin karatu irin hakan ke sa wasu Iyayen yara shiga wani hali domnin basu daɗe da dawowa daga hutu ba, bayan bukukuwan da aka yi,wanda sanin kowa ne ana kashe magudan kuɗaɗe.

Ya yin da aka buɗe makaranta, yawancin iyaye suna fuskantar irin yadda zau ɓullowa abubuwan da suka zama dole ne sai an saye su kafin ƴaƴan nasu su samu koma makaranta. Sai dai wasu Iyayen suna waɗansu buƙatunsu ne,ko kuma ɗaukar lokaci kafin su yi wani abin, har ma wasu buƙatun gida ana rage su, wasu kuma suna rancen kuɗi ne ko kuma yin wasu ayyuka can daban, wannan ya nuna a fili yadda saye- sayen kayan makaranta kuɗaɗen suka fi na makaranta.

Yawancin Iyaye su ba ma yawan kuɗaɗen da ake kashewa suka dame su ba, babbar damuwar ita ce tashi da sassafe domin a shiryawa yara abinci, akwai maganar kai su makaranta, ta motar haya, wanke kayan makaranta, ga maganar kitso na ƴan mata wamda yake ɗaukar mako biyu, akwai kuma wasu ayyukan gidan. Da kuma lokacin da ake ɓatawa ana yin wasu daga cikinin abubuwan da sua kamata, shi yasa lamarin komawa makaranta ba ƙaramin abu bane da yake tada hankalin yawancin waɗanda ƴaƴansu ke zuwa makaranta.

Kamar yadda kalandar komawa makarnta ta mkarantun gwamnati da waɗanda ke zaman kansu wato Firamare da Sakandare, a Jihohin Ogun da Delta sun koma ne ranar 5 ga Janairu 2026 shekarar karatu ta 2025/2026 ranar Litinin, yayin da wasu Jihohi da suka haɗa da Legas za su koma makarantar wani lokaci a wannan watan na Janairu.

A Abuja Malaman makaranta sun dawo hutu ne makon daya gabata saboda su samu horo na shiryawa kafin komawar ƴan makaranta kafin ko kuma ranar 11 ga Janairu, 2026.

Iyaye waɗanda suka tattauna da LEADERSHIP Lahadi sun bayyana irin matsalolin da suke fuskanta na kuɗi saboda shirya ma komawar ƴaƴansu sabon zangon karatu. Yawanci suna faɗi- tashi ne suga yadda lamarin zai kasance duk kuwa da yake kuɗaɗen shigar suna da wuya ga kuma tsadar rayuwa.

Ga wasu iyalan, kuɗaɗen da suka kashe sun haɗa da tafiye- tafiyen da suka yi saboda bukukuwan Kirsimati da sabuwar shekara, abin ya haɗa da zurga- zurga da kuma wurin kwana, wanda wani abu ne idan lokacin komar makarantar ƴaƴansu ta yi wato irin matsin da su kan shiga.

Duk da yake dai wasu Iyayen suna nuna abin kamar bai dame su bane, sai dai kowa ya sani idan ana maganar komawa makaranta ne, abin yana laƙume babbar lalitar gidan, abinda kuma ba ƙaramin tasiri yake da shin a babbar matsalar da dole ne sai an yi maganinta.

Ga Mrs.Grace Collins, mahaifiyar ƴanmakaranta biyu daga Lugbe,ta ce lamarin kuɗi da matsalar da ake shiga lokacin komawa makaranta abin mai zaman kan shi ne.Ƴaƴanta na zuwa makarantar kuɗi ne inda kuɗin makarantar kaɗai Naira 150,000 ga kowane yaro duk farkon zangon karatu, irin waɗannan kuɗaɗen sun wasu iyalai ƴan Nijeriya a matsayin kuɗin shigar da suke zuwa masu kowane wata.

Ta ce bayab hakan, dole ne ta biya Naira120, 000 saboda motar makaranta domin ta tabbatar da cewaƴaƴanta suna zuwa makaranta babu wata matsala su je su dawo.

“Lamarrin kuɗin motar zuwa makaranta abin ya fi damunmu ƙwarai. Za ka biya Naira 150,000 wanda ana saran zaka biya, bayan haka akwai wata Naira 120,000 domin kuɗin motar da za’a riƙa zuwa makaranta,na wasu watanni, ni ina ma tunanin muna kashe kuɗi ne da yawa saboda kawai a riƙa kai su zuwa makaranta domin su samu ilimi kamar yadda ta ce.

Hakanan ma da akwai ƙarin wasu kuɗaɗe,kamar, akwai na ci gaba, gudunmawa ta ƙungiyar Iyaye da ɗalibai, kuɗaɗen jarrabawa, kuɗin kayan makaranta, waɗannan sun ƙara kuɗaɗe fiye da na makaranta.

Ga sauran Iyayen Dutse, Jabi, Nyanya, Karu, and Kubwa, irin kuɗaɗen da suke kasewa babbar matsala ce.Mrs. Geɓolor Itam da ke Jikwoyi, ta bayyana cewa biyan Naira 150,000 ake biya ma kowane yaro a matsayin kuɗin makaranta, ga kuma Naira 135,000 kuɗin mota mai kai ƴan makaranta “muna biyan kuɗaɗe da yawa domin mu ilimantar da su.”

Sai kuma a Jabi, wata mata mai ƴaƴa uku Mrs Salamatu Ibrahim da ke a Sabondele Plaza ita ma ta bayyana irin matsalar da take fuskanta,“Kafin ma, a koma makarantar kamar yadda ta ce, tuni aljihunanmu sun yi ƙasa inda muke biyan kuɗin, Littattafai, da na zurga- zurga. Gaskiya abin ba’a cewa komai.”

A Nyanya, Akwai wani mutum mai ƴaƴa huɗu mai suna, Mista. Amadi Saɓiour ya ce, “Kuɗin da ake biya zuwa makaranta a motar fasinja da kuma sauran buƙatoci hakan ya maida ilimin ƴaƴanmu ya kasance tamkar wani babban abinda zai faranta masu rai, har ya zama ko ta halin ƙaƙa sai mun samar masu da shi.Muna biyan kuɗaɗen yin wasu abubuwa ”

Iyaye a Karu da Kubwa su ma haka suke kallon al’amarin da irin ban takaici,musamman yadda suke la’akari yadda kuɗaɗen suke da wuyar zuwa/samu ta ɓangare ɗaya kuma tsadar rayuwa wanda har ya sa muke yi lamarin tamkar da ba zai yiyu bane.Yawanci basu samun isasshen bacci da dare ga kuma damuwa, yayin da suke ta yin faɗi– tashi su, ga hanyar da za su ɓullo ma abubuwa biyu wato abubuwan da ake buƙata gida, da kuma buƙatun komawa makaranta.

Sauran Iyaye suna tunanin yadda kuɗin makaranta na makarantu masu zaman kansu suke ƙaruwa sannu a hankali a shekaru goma da suka gabata,sauran wuraren da ke buƙatar sun haɗa,zurga- zurga zuwa makaranta,sai kuma kuɗaɗen za ‘a ware su ne domin haɗu da abubuwan ba ayi zato ba,ƙaruwa suke ci gaba da yi bama kamar idan aka yi la’aki da hauhawar farashin kaya da tsadar hakan ne ya ƙara ɓatawa yadda Iyaye suka yi kasafin kashe kuɗaɗensu.

Abin ya wuce kamar yadda aka samu labarin ake yi. An samu bayanin yadda Iyaye suke amfani da kuɗaɗen da iyalai ke tarawa, suna mantawa da muhimman abubuwan da suka kamata ayi na gida, ko ma a taɓa kuɗaɗen da aka aje domin kula da lafiya ko wasu abubuwa can daban, domin a ga cewar lalle an biya buƙatun komawa makaranta.

Wani abinda ya kasance tamkar yana gidan kowa a lamarin iyalan Nijeriya shi ne matuƙar an fara sabon zango na karatu, gani suke kamar ranar ce za su fara koyon yadda ake tara kuɗi ne duk yadda suka kasafta yadda za su kashe su.

Wani mutum mai suna Titus Tor a Abuja, da ɗansa ke karatu a Makantar Sakandaren gwamnati ta Wuse, ya yi magana ne kan irin kuin da yake kashewa kowace rana kan kuɗin mota.

“Ina zama ne a Lugbe, ina kashe fiye da Naira 2,500 kowace rana kan kuɗin mota da nake biya ma ɗana.Wannan ba ƙaramin abu bane ga mutum irin’’.

“Ina son gwamnati ta shigo cikin lamarin kuɗin zurga- zurga domin a sauƙaƙawa Iyaye waɗanda makarantarsu nesa take kan irin halin da suke shiga. Hakan yana shafar mu na kaɗan ba.”

Ita ma a nata bayanin, Mrs Theresa Moji, da ƴarta ta ke Makarantar kwana ta mata da ke Benuwe, abin yana matauƙar damunta domin ya zarce kuɗin makaranta, saboda tana kashe fiye da Naira 200,000 kan kayayyakin da ƴarta take amfani da su a makaranta.

“Mijina Malamin makarantar Firamare ne.Yadda muke tara kuɗin, bayan fiye da Naiar 300,000 kuɗin makaranta, muna fuskantar wahala kafin ace mun samu kuɗin.

“Farkon owane zangon karatu muna kashe fiye da Naira 200,000 kan kayan da muke sayar ma ƴarmu da sauran wasu abubuwa. Wannan babbar matsalar da muke fuskanta mu iyaye masu ƙaramin ƙarfi a faɗin Nijeriya.”

A wurare daban daban, lamarin kuɗin da ake kashewa kan ilimi ba ɓoye yake ba, kamar kuɗin zirga- zirga, kayan makaranta,da sauran abubuwa abin ba ƙaramar wahala masu ƙaramin ƙarfi ke yi ba, har abin wani lokaci ya kan bar iyalai tambayar kansu yay a za ayi su iya tafiya da buƙataun kalandar harkoin makaranta?.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *