Fiye da tsageru 80 sun ajiye makamai a Kuros Riba

[ad_1]



Fiye da tsageru 80 a Jihar Kuros Riba sun miƙa makamansu tare da yin watsi da ayyukan ta’addanci, a wani biki na musamman da aka gudanar a ranar Juma’a a ƙananan hukumomin Akpabuyo da Calabar ta Kudu.

Bikin miƙa makaman, wanda aka gudanar a Atimbo, ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Rundunar Sojin Birged ta 13 tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro na Operation Okwok, inda tsagerun suka miƙa wuya tare da miƙa makamai ga jami’an tsaro cikin kwanciyar hankali.

Rahotanni sun nuna cewa mayaƙan sun riƙa zuwa rukuni-rukuni suna miƙa makamansu, lamarin da jami’an tsaro suka bayyana a matsayin babbar nasara wajen dawo da zaman lafiya a yankin.

Daga cikin waɗanda suka miƙa makaman akwai rukuni na mayaƙa 39 ƙarƙashin jagorancin ThankGod Ebikontei, wanda aka fi sani da Ayibanuagha, da kuma wani rukuni na biyu na mayaƙa 41 ƙarƙashin jagorancin John Isaac, mai laƙabi da Akpoko, wanda shi ne kwamandan ƙungiyar Akpokolo Marine, da aka fi sani da Border Boys.

Aminiya ta tabbatar da cewa makaman da aka miƙa sun haɗa da bindigogi ƙirar AK-47, G3, harsasai, abubuwan fashewa, da kuma ƙananan jiragen ruwa masu saurin gaske.

Da yake jawabi a wajen bikin, Kwamandan Rundunar Sojin Birged ta 13, Brigadiya-Janar P. O. Alimikhena, ya bayyana farin cikinsa kan yadda tsagerun suka rungumi zaman lafiya tare da ajiye makamai.

Ya ce babu wani abu da ya fi zaman lafiya daraja, yana mai jaddada cewa daina ayyukan ta’addanci da rungumar zaman lafiya abin a yaba ne matuƙa.

Brigadiya-Janar Alimikhena ya yi kira ga tsoffin tsagerun da su tabbatar da aniyarsu ta ɗorewa kan zaman lafiya, tare da gargaɗinsu kan komawa ga ayyukan assha.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *