Sin: Tattaunawa Da Diplomasiyya Na Da Muhimmanci Wajen Samun Zaman Lafiya Mai Dorewa

[ad_1]

Babban jami’in kasar Sin a ofishinta dake MDD, Sun Lei, ya ce ba za a taba samun zaman lafiya mai dorewa ta hanyar nuna karfin iko ko matsin lamba ba, sai dai ta hanyar tattaunawa da diplomasiyya.

Da yake jawabi jiya Juma’a ga taron tattaunawa kan Cikar Kundin Tsarin MDD Shekaru 80: Sake Fasalta Hanyoyin Kandagarki da Warware Rikici, Sun Lei ya ce duniya ta shiga wani sabon yanayi na hargitsi da sauye-sauye, inda yanayin tsaro a duniya ke kara zama mai sarkakiya da karuwar take dokokin da kundin tsarin MDD ya tanada. Ya ce dole ne a fahimci wani abu guda, wato kalubalen da ake fuskanta yanzu ba su da nasaba da dadewar kundin tsarin, sai domin rashin girmama dokokin da ya tanada.

Sun Lei ya kuma nanata muhimmancin tsayawa kan tattaunawa da tuntubar juna. Yana cewa, ya kamata kasashe su girmama ‘yancin kan juna da iko da yankunansu, su kuma dauki damuwar tsaro da kowannensu ke da ita da muhimmanci da kuma karfafa aminci a tsakaninsu.

Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da hada hannu da kasashen duniya wajen daukaka kundin tsarin MDD da goyon bayan warware sabani cikin lumana da kuma bayar da karin gudunmuwa ga zaman lafiya da ci gaban duniya. (FMM)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *