Kotu ta dakatar da yunƙurin tsige Fubara




Wata babbar kotu a Jihar Ribas, ta bayar da umarnin wucin-gadi na dakatar da yunƙurin tsige gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa, Ngozi Nma-Odu.

Kotun, wadda ke zaman ta a Fatakwal, ta umarci kakakin majalisar dokokin jihar, Martin Amaewhule, da wasu da ake ƙara a shari’ar, da su dakatar da duk wani mataki na tsige gwamnan.

Cikin waɗanda aka hana akwai akawun majalisar dokokin da kuma alƙalin alƙalan jihar.

Hakazalika, kotun ta hana alƙalin alƙalan jihar, Mai Shari’a Simeon Chibuzor-Amadi, karɓar ko duba kowane ƙorafi ko buƙata da ta shafi tsige gwamnan, na tsawon kwanaki bakwai.

Gwamna Fubara da mataimakiyarsa ne, suka shigar da ƙara a kotu, inda suka nemi a dakatar da yunƙurin tsige su.

Jihar Ribas dai ta daɗe tana fama da rikicin siyasa tun bayan zaɓen 2023.

Rikicin ya kai ga Shugaba Bola Tinubu dakatar da gwamnan na tsawon watanni shida a shekarar da ta gabata.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *