Yadda na zama almajirin Maitatsine don tsira da raina
Shekaru arba’in da biyar bayan rikicin Maitatsine ya jefa Kano cikin firgici, har yanzu tabonsa na nan a zukatan waɗanda suka shaida wannan lokaci.
A yau, Aminiya ta kawo muku ci gaban labarin da ta wallafa a baya kan rikicin Maitatsine, a wannan karon daga bakin guda daga cikin almajirin Malam Muhammad Marwa (Maitatsine), wanda ya yi yaƙi tare da shi da sauaran mabiyansa, amma ba don son ransa ba, sai don tsira da ransa.
Malam Abdullahi Jafar, wanda aka fi sani da Abdullahi Ɗan Fagge, haifaffen yankin Bichi ne a Jihar Kano, wanda almajiranci ya kawo shi unguwar Fagge da ke birnin Kano tun kafin a kafa ƙaramar hukumar.
Abin da ya gani a lokacin rikicin Maitatsine ya sa har yanzu, bayan shekara 45, idan yana ba da labari, zuciyarsa kan cika da nadama.
“Malaminmu shi ne Malam Saleh. A wancan lokaci bisa al’ada idan baƙo ya zo, yana tambayar makarantar ’yan garin, sai a nuna masa. To a lokacin a unguwar ’Yan Awaki, daga makarantar Sakkwatawa sai ta ’Yan Tatsine a girma.
“Su ’Yan Tatsine tasha-tasha suke bi, daga sun ga ka sauke adakarka irin ta da, za su ce makarnata kake nema, da ka ce eh, sai su kai ka makarantar Maitatsine.
“Da haka suka tara almajirai bila-adadin har suka dinga zuwa shagunan mutane bayan canza wa Kasuwar Kwari matsuguni da gwamnan lokacin, Margayi Abubakar Rimi ya yi,” in ji shi.
A cewarsa, ƙungiyar Maitatsine ta yi amfani da wannan salo wajen yaudarar almajirai. Ta haka ne kuma suka tara almajirai babu adadi.

Yadda muka faɗa a hannun ’Yan Tatsine
Bayan kisan ɗan Maitatsine mai suna Tijjani da ake kira da Kan’ana, Abdullahi na cikin waɗanda rayuwarsu ta canja baki ɗaya. A lokacin yana da kimanin shekaru 20 a duniya.
“Bayan kashe Tijjani sun binne shi a Maƙarbartar Abbtuwa… Duk wanda ya shiga gida a wannan ranar sai da aka shiga aka fito da shi, mace kuma idan da ƙwarinta sai a kai ta gidan Maitatsine.”
Ɗan Fagge da abokan karatunsa su 30 da malaminsu, Malam Saleh, sun nemi taimakon maƙwabcinsu Alhaji Yawale, saboda yanayin gidan da suke ciki na rashin abinci da ƙofa mai ƙarfi.
Sai dai bayan fitowarsu da zummar barin unguwar tare da Alhaji Yawale da iyalinsa, sai ’Yan Tatsine suka tisa su a gaba har gidan Maitatsine.
“Da asuba sai suka zo suka kira Alhaji Yawale. Suka tambaye shi shin ba ka son Malam na yaƙi ba ne? Ya ce na sani. Sai suka ce me ya sa ba ka kawo masa taimako ba? Sai ya ce ai bai san yana so ba. Sai suka tafi da shi amma daga nan bai dawo ba.”
“Sai aka tafi da Malam Saleh. Shi ma bai dawo ba. Haka sauran manyan da sai ya rage saura matasa irina.
Yadda ’yan Tatsine ke wa almajirai kisan gilla
Ɗaya daga cikin abubuwa mafiya firgitarwa a labarin Ɗan Fagge shi ne yadda ya shaida kisan gillar da aka yi wa yara irinsa da malaminsu a kan idonsa.
“Muna zaune sai ga su sun shigo da sharɓeɓiyar adda, duk jini a jikinta. Ba yanka mutum suke yi ba, wani ice ne suke maka wa mutum ya faɗi sai su hau shi da sara da adda a wuya har sai ka mutu.
“A haka aka kashe fiye da almajirai 30, ciki har da ’ya’yan manyan unguwa da malamai,” in ji Abdullahi.
‘Dalilin da na bi Maitatsine’
Abdullahi Ɗan Fagge bai bi Maitatsine saboad ya yarda da shi ba. Ya bi shi ne domin ya tsira da ransa, a cewarsa.
“Sai da aka zo kaina ni ne na ƙarshe. A cikin tsoro da kuka na roƙe su na ce don Allah ko da kun kashe ni, ku bai wa malam Musa Ƙur’anina. Ban san shi ba kawai na faɗi sunansa ne.
“Sai suka tambaye ni wane ne ni? Na ce daga Maiduguri na zo karatu ni almajiri ne. Sai suka ce me ya sa ba ka faɗa ba? Na ce na faɗa ba su yarda da ni ba ne. Sai aka kai ni gaban Maitatsine da kansa.
“Sai ya dinga haska ni da fitila. Sai ya ce ku shaida wannan almajirina ne har sau uku.” Sai suka ce ‘mun shaida ya annabin Allah!’.”
A nan ne aka tilasta masa shiga ayarin. Aka ba shi makamai, aka fitar da shi fagen daga.

Yaƙin ƙarshe tare da Maitatsine
Yayin da gwamnati ke amfani da makamai na zamani da suka haɗa da bindigogi da igwa da hayaki mai sa hawaye, su kuma ana tura su ne da adduna da kwari da baka.
Da Abdullahi ya ga tashin hankalin ya yi masa yawa, sai ya ce ba shi da lafiya.
A haka aka mayar da shi aikin jinya, yana wanke jini, yana ɗaura bandeji, yana kallon rayuka suna salwanta.
Lokacin da sojoji suka kai hari gidan Maitatsine, sai suka fara gudu. Sai ya umarce su da kada su waiwaya, su yi ta gudu kawai. A haka aka harbe shi a ƙafa, sai suka haɗa gadon kara da suka samo katakan daga wani gida da ke kan hanya, suka ɗauke shi.
A nan Ɗan Fagge ya rabu da su shi da wasu mutane bakwai. Sai dai mutum shida ƙone su aka yi, yayin da shi kuma ya tsira bayan hayewa bishiya da ya yi.
Da magariba ta yi, ya sauko, yunwa da ƙishirwa sun galabaita shi.

Bayan rikicin
An kai shi gaban kwamitin da Gwamnatin Tarayya da ta jiha ta kafa domin bayar da bayani, amma magana ta gagare shi. Kuma ko da tallafin gwamnati ya zo, bai karɓa ba.
“Allah Ya dauke min magana sai kuka kawai nake yi. Idan ka je sai ka rantse sannan ka karɓa. Amma gaskiya ban je ba, ban nema ba.”
A ƙarshe, Ɗan Fagge ya bayyana abin da ya ƙara tabbatar masa da cewa aƙidar Maitatsine ba Musulunci ba ce.
“Dangane da batun Sallah kuwa… ban taɓa ganin sun yi ba, sai sau ɗaya. Shi ma ba irin yadda ake yi ba. Babu kabbara babu komai. Sai wajen fadar ‘rabbana wa lakal hamdu, sai su ce rabbana wal wal hamdu.” Ni ma saboda ƙuruciya a lokacin ba na yi.
Ɗan Fagge ya kuma ce su ne asalin aƙidar ‘Ƙala Ƙato’ saboda ba su yarda da Hadisan Annabi ba (SAW), shi suke ce wa ƙato, Maitatsine ne annabinsu. Domin Annabin ma suke kiran sa.