Katsina United ta koma mataki na 8
[ad_1]
Kungiyyar ƙwallon ƙafa ta Katsina United ta matsa zuwa mataki na 8 a saman teburin gasar Firimiyyar Nijeriya bayan doke Kun Khalifat 2-0 a wasan mako na 20.
Ɗan wasan gaban kungiyyar Jamilu Yusuf ne ya zura ƙwalleyen biyu, ta farko a minti 48, sai ta biyu a minti 78 bayan, an dawo daga hutun rabin lokaci.
Da wannan nasarar ƙungiyyar ta koma mataki na 8 da maki 29 iri ɗaya da na Niger Tornadoes da Bendel Insurance da ke mataki na 6 da 7.
Yanzu haka dai Katsina United na da kwantan wasa tsakaninta da Enugu Rangers, idan kuma ta samu nasara zata iya komawa mataki na huɗu a saman teburin.
Ƙungiyyar ta buga wasanni 19, nasara 8, kunnen doki 5 aka kuma doke ta a wasanni 6.
A ranar Lahadi mai zuwa United za ta yi tattaki zuwa birnin Delta domin buga wasan mako na 21 da Warri Wolves.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link