Antoine Griezmann ya ci ƙwallo 200 a Atletico

[ad_1]



Fitaccen ɗan wasan gaban Atletico Madrid, Antoine Griezmann ya kafa tarihin zama na farko a ƙungiyar da ya ci mata ƙwallaye 200.

Griezmann ɗan asalin Faransa ya kafa wannan tarihin ne a ranar Talata yayin Gasar Zakarun Turai, inda Atletico ta lallasa Eintracht Frankfurt ta Jamus da ci 5-1.

Kocin Atletico, Diego Simeone ya bayyana farin cikinsa kan ƙwazon ɗan wasan, inda yake cewa “ba ruwan hazaƙa da shekaru.”

Griezmann mai shekaru 34, ya kwashe kusan shekaru 10 a Atletico kafin ya cim ma wannan mataki.

A cewar Simeone, “ina godiya ga Antoine da lokacin da ya kwashe a Atletico Madrid. Ya ci ƙwallo 200, wanda abin al’ajabi ne.”

A ƙarshen kakar bara, an yi ta raɗe-raɗin Antoine Griezmann zai bar ƙungiyar, amma sai ya tsawaita kwantiraginsa zuwa 2027.

Sai dai a kakar bana, mintuna 416 kawai ya buga zuwa yanzu a wasanni tara, inda yake yawan shigowa wasa daga benci.

A halin yanzu, a kakar bana ana hasashen Griezmann zai zama ɗan Atletico na huɗu da ya buga mata wasanni 500, bayan Adelardo, da Koke, da kuma Jan Oblak.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *