Binciken Jin Ra’ayin Jama’a Na Cgtn: Duniya Na Maraba Da Shawarar Sin a Bangaren Inganta Tsarin Shugabancin Duniya

[ad_1]

A farkon wannan shekara, tsarin shugabancin duniya yana fuskantar kalubale mai tsanani. Binciken jin ra’ayin jama’a na tsawon shekaru 2 da CGTN ta gudanar, tare da jami’ar Renmin ta Sin a kan mutane 31,000 daga kasashen duniya 52 ya nuna cewa, kashi 70.6 cikin 100 na masu bayyana mahanga sun yarda cewa, tsarin shugabanci na manyan kasashe masu wadata ya gaza. Kana kashi 71.6 cikin 100 na ganin cewa, babu adalci a dokokin kasa da kasa na yanzu, yayin da suka aza ayar tambaya kan ingancin MDD.

Dukkanin masu bayyana ra’ayoyin na maraba da shawarar kasar Sin. Kashi 74.8 cikin 100 daga kasashe masu tasowa sun amince da manufar “kafa kyakkyawar makomar bil’adama ta bai daya”, yayin da kuma ra’ayin “tattaunawa, da samun ci gaba cikin hadin gwiwa, da raba damammaki tare” ya samu karbuwa sosai. Kashi 69 cikin 100 sun amince da gudunmawar da Sin ke bayarwa a bangaren gudanar da harkokin duniya, yayin da kashi 67.1 cikin 100 suka yi fatan Sin za ta kara taka muhimmiyar rawar a zo a gani. Sassan masu bayyana ra’ayi a binciken sun hade dukkanin sassan kasa da kasa, kuma sakamakon ya yi daidai da mahangar akasarin jama’ar duniya. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *