CAF ta dakatar da Samuel Eto’o wasanni huɗu da cin tara
[ad_1]
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta nahiyyar Afirka CAF ta dakatar da shugaban hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Kamaru, Samuel Eto’o wasanni huɗu da kuma tarar dala 20,000 bisa zarginsa da rashin ɗa’a a wasan da Kamaru ta doke Morocco a wasan gab da kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin Afrika.
CAF ta ce Eto’o ya nuna rashin ɗa’a ga Alƙalan wasa da kuma shugabanta, Patrice Motsepe.
Ana ta ɓangaren hukumar ƙwallon ƙafa ta Kamaru FECAFOOT ta karɓi hukuncin amma ta soki tsarin, ta sha alwashin ɗaukaka ƙara, tare da jaddada goyon bayanta ga Eto’o.
Haka zalika CAF tabbatar da cewa, tana gudanar da bincike kan cece-kucen da aka samu a filin wasa yayin karawar da aka gudanar.
Kawo yanzu dai Morocco mai masaukin baki za ta ƙara da Senegal a wasan ƙarshe, yayin da Najeriya za ta ƙara da Masar a wasan neman gurbi na uku a gasar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link