’Yan Bindiga Sun Sace Shanu 500 A Kasuwar Zamfara

[ad_1]

’Yan bindiga sun sace shanu aƙalla 500 a Kasuwar Daji da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara.

Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Ƙasa (CBAN) a jihar, Aminu Garba ne, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ba wannan ne karo na farko da aka kai hari kasuwar ba.

  • Kotu Ta Janye Tuhume-tuhumen Da Ake Yi Wa Sanata Natasha
  • ‘Yansanda Sun Cafke Mutum 2 Bisa Zargin Luwaɗi Da Ƙananan Yara A Bauchi

Ya bayyana cewa ’yan bindigar sun zo kasuwar da rana inda suka sa ido kan yadda harkoki ke gudana sannan suka kai harin cikin dare.

Shanun da aka sace an tara su ne daga kasuwanni daban-daban, ciki har da wasu daga Jamhuriyar Nijar.

Garba ya ce kasuwar ba ta da katanga, abin da ya bai wa ’yan bindigar damar tserewa zuwa daji cikin sauƙi, duk da cewa suna da yawa kuma ɗauke da makamai masu yawa.

Ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, Alhaji Sani Yaba Ajiyan Fawa, ya ce sama da ’yan bindiga 100 ne suka kai harin.

Ya ƙara da cewa an samu nasarar ƙwato shanu kusan 60 bayan sun watse yayin kai harin.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, ’yansanda ba su fitar da wata sanarwa kan harin ba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *