Cinikayyar Sin Da Afirka Ta Bude Sabon Babi

[ad_1]

Hukumar kwastam ta kasar Sin, ta fitar da wasu bayanan cinikayyar shige da fice ta Sin na shekarar 2025 a jiya Alhamis. Alkaluman na nuna cewa, darajar cinikin shige da fice tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka, ya kai yuan tiriliyan 2.49, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 357.076, adadin da ya wuce dala biliyan 300 a karon farko, kana ya karu da kashi 18.4 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabaci hakan. Daga cikin kasashe 64 na Afirka da Sin ke cinikayya da su, yawan karuwar ciniki da kasashe 41 ya kai fiye da kashi 10 cikin 100, yayin da kasashe 22 suka samu karuwar fiye da kashi 30 cikin 100.

A bangaren shigo da kayayyaki, Sin tana aiwatar da matakin janye haraji kashi 100 cikin 100, kan kayayyakin da ake shigar da su kasar, daga kasashe 53 na Afirka masu huldar diplomasiyya da ita, don fadada shigo da kayayyakinsu cikin gidanta, da kuma raba fa’idar babbar kasuwar Sin. Wannan ya sa kayayyakin amfanin gona masu karin daraja irin su avocado na Kenya, da kofi na Habasha, da lemun tsami na Afirka ta Kudu, samun damar kara shiga kasuwar Sin, wanda hakan ke amfanar da manoma, da kananan kamfanoni na Afirka.

A bangaren fitar da kayayyaki, kayayyakin da Sin ke fitarwa zuwa Afirka ya inganta sosai. Inda cinikin wasu kayayyaki masu kunshe da fasahar zamani, irin su sabbin motoci masu amfani da wutar lantarki, da na’urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana, da batirin lithium, ke cikin wani yanayi na karuwa. Ban da haka, kayayyakin Sin suna taimakawa wajen inganta masana’antu, da kuma yunkurin karkata zuwa sabon salon bunkasa ba tare da gurbata muhalli ba a Afirka.

Bayanan cinikayya na shekarar 2025, takarda ce mai nauyi da ke bayyana nasarorin da aka samu, kuma takardar ta fayyace alkawarin da Sin take cikawa, na samun ci gaba tare da kasashen waje, har ma takardar ta sanar da makoma mai haske a nan gaba. Kazalika, ta bayyana hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, da dogaro da juna, da daidaito, da cin moriyar juna, da daukar ainihin matakai, wanda hakan ke taimakawa wajen habaka tattalin arzikin duniya, da kuma kyautata tsarin shugabancin duniya.

Tattaunawa tsakanin Sin da kungiyar tarayyar Afirka ta AU kan manyan tsare-tsare da aka kammala a kwanan nan, ya tabbatar da karfafa hadin kai tsakanin shirin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 15, da shirin “Raya Afirka nan da 2063” na AU, wanda hakan shaida ce mafi kyau ga yunkurin bangarorin Sin da Afirka na samun ci gaba tare.

Idan an yi hangen nesa, za a ga cewa kasar Sin da kasashen nahiyar Afirka, bisa hadin gwiwarsu za su kirkiro wani sabon tsari na tattalin arzikin duniya, mai tabbatar da daidaito da wadata tsakanin dimbin bangarori masu fada-a-ji. (Mai rubuta: MINA)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *